INEC za ta fara sabon aikin rajistar masu zaɓe a farkon 2021

0

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ce za ta soma wani sabon aikin yi wa masu zaɓe rajista a cikin watanni uku na farko na shekarar 2021.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, shi ne ya bayyana haka ga manema labarai a Abuja a ranar Laraba bayan ya bayyana a gaban Kwamitin Hukumar Zaɓe ta Ƙasa na Majalisar Dattawa domin ya kare kasafin kuɗin hukumar na shekarar 2021.

A cewar sa, za a yi aikin yin rajista har zuwa watanni shida kafin a yi manyan zaɓuɓɓukan shekarar 2023.

Ya ce, “Za mu ci gaba da gudanar da aikin yin rajistar masu zaɓe a watanni uku na farkon shekarar 2021. Kuma da zarar mun ci gaba, aikin zai ci gaba babu tsayawa har zuwa shekara ɗaya da rabi, aƙalla watanni shida kafin a yi manyan zaɓuɓɓukan da ke gaba.”

Haka kuma ya bayyana cewa a yanzu haka hukumar ta na fafatawa a ƙararraki kamar 1,700 na kafin zaɓe da bayan zaɓe da aka kai kotu daga zaɓuɓɓukan shekarar 2019.

Sai dai kuma ya ce hukumar ba ta biyan lauyoyi manyan kuɗaɗen shari’un da ake yi amma ta na dai biyan kuɗaɗen da Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya ta ƙayyade.

Farfesa ya ce, “Misali, idan mu na da shari’a daga zaɓen gwamna a Kotun Ƙoli, kuɗi mafi yawa da za mu biya lauyoyi shi ne naira miliyan 4.5, amma saboda yawan shari’un mun kusa samun ƙararraki har guda 1,700 na kafin zaɓe da na bayan zaɓen shekarar 2019 kaɗai.

“A ko yaushe za ka ji mutane su na zuwa kotu tare da haɗa INEC a ƙarar su, amma mu dai za mu ci gaba da yin abin da za mu iya ne da iyakar abin da ke aljihun mu.”

Tun da farko a jawabin sa ga Majalisar Dattawan, Farfesa Yakubu ya ce hukumar ta tsara za ta ɗauko kuɗi naira biliyan 5.2 daga asusun ta na naira biliyan 10 ta haɗa cikin kasafin ta na shekarar 2020.

See also  Karanci sabbin kuɗi: Mutane Hudu Sun Mutu a Zanga-Zanga a Jihar Edo

Ya ce hukumar ba ta taɓa kashe ko kwabo ba daga wannan asusun tun da aka kafa ta a cikin 2010, yayin da ya ce dalilin da zai sa a ciro kuɗin shi ne saboda rage mata kuɗi da aka yi a kasafin shekarar 2020.

Ya ce, “Abin da ya faru yanzu shi ne kasafin mu na shekarar 2020 ya yi ƙasa da naira biliyan 40 daga naira biliyan 45.5 a shekarar 2019.

“Saboda kashi 10 cikin ɗari na kuɗin da aka zabtare saboda annobar korona, sai kuma kuɗin su ka ƙara raguwa zuwa naira biliyan 36 a tsakiyar shekarar a lokacin da mun riga mun gama shirye-shiryen kashe kuɗaɗen.

“Saboda haka, tunda dai an yi asusun ne saboda lokaci irin na yau da ake buƙatar sa, na sanar da kwamitin cewa ranar buƙatar kuɗin ta zo.

“Don haka, za mu ciri wani sashe na kuɗin asusun domin mu yi balas da kasafin mu na bana.”

A kan batun bai wa ‘yan Nijeriya mazauna ƙasar waje damar yin zaɓe a inda su ke, shugaban ya ce hakika hukumar ta na son ganin ta ba su dama su yi zaɓe, amma tabbatar da yiwuwar hakan ya na buƙatar a yi wa tsarin mulki da kuma Dokar Zaɓe garambawul.

Ya ce, “Mun riga mun gama tsara takardun, da zarar an gyara dokar, to za mu iya fara aiwatarwa.

“Mun gama shiri, mun yi zama da dama da su ‘yan Nijeriya a Hukumar Mazauna Ƙetare, wato Diaspora Commission (NIDCOM), amma ba za mu iya tsallake abin da doka ta tanadar ba.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here