Iran ta yi babban kamu.

0

Nasir Isa Ali
Iran ta yi babban kamu.

Ma’aikatar leken asiri na Iran ta bayyana cewar,ta sake samun gagarumar nasara, domin kuwa ta sake cafke wani kasurgumin dan ta’adda mai kare muradun Amurka,kuma mazaunin a kasar ta Amurka.

Bayanan sun bayyana cewar,lallai wannan kamun tamkar wani naushi ne a fuskar gungun yan ta’adda masu goyawa Amurka baya. Takardar tace “Shugaban kungiyar nan mai suna”TONDAR” (Thunder) ya shiga hanun jami’an leken asirin Iran.

Ma’aikatar leken asirin tace zata yi karin bayani nan gaba kadan,domin suna can suna matse shi domin samun karin bayanai da haske.

A watannin baya Iran din,a wani salo mai ban al’ajabi,ta samu nasarar cafke Mr. Rohollah Zam,wani dan Iran mazaunin kasar Faransa,wanda kuma kasashen Amurka,Faransa,Israila da Saudiya ke daukar nauyinsa tare da bashi kariya.

Nasir Isa Ali

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here