Iyalan mai tattaunawa da yan ta’adda don ceto mutane, Tukur Mamu sun yi martani kan kayan sojoji da aka gano a gidansa suna mai cewa na dansa ne, jami’in sojan ruwa.
Hakan na cikin wata sanarwa ne da Ibrahim Mada ya fitar kuma ya raba wa manema labarai a Kaduna, Wanda Nigerian Tribune ta rahoto.
Iyalan kuma sun yi kira ga DSS su dena yi wa Mamu, mawallafin jaridar Desert Herald da ke Kaduna kazafi a shafukan watsa labarai’.