JAM IYYAR APC. A JAHAR KATSINA NA TSAKA MAI WUYA

0

JAM IYYAR APC. A JAHAR KATSINA NA TSAKA MAI WUYA

Daga wakilan Taskar labarai

Fushin fitar da Dan takarkaru a jam iyyar APC a Katsina yanzu ya Sanya ta a tsaka mai wuya.inda wadanda ba suyi nasara ba ,suke zargin uwar jam iyya ta jaha da gwamnatin jaha wajen kayar dasu.

Akan Haka mafi yawansu suka kafa wata kungiya wadda suka ce .sai sun Mai da martani Mai zafi akan abin da akayi masu

Anyi Zama dasu a ranar Alhamis da ta gabata inda aka Basu hakuri kuma aka roke su da cewa su manta a fuskanci gaba aka kuma gargade su da cewa ..ba za a amincewa kafa wata Kungiya ba.a cikin jam iyya

Gwamnan Katsina, a ,zaman har wani gargadi yayi…Akan cewa duk Wanda baya iya hakuri Kofa a bude take ..Domin rufe Kofa da munafuki tafi komai hatsari. ..

See also  Gwamna Radda ya karbi bakuncin kwamitin majalisar dattijai ta kasa kan ayyukan jami'an kwastam musamman a titin Katsina-Jibia

A taron da akayi wani mahalarci ya kalli shugaban APC na Katsina shittu s shittu..yace Masa Kai Ku kune matsalar jam iyyar nan.ta APC a Katsina

Wannan gargadi ..kar a kafa kungiya sun bi ta Bayan kunnen mahalarta taron..Domin suna fitowa suka ce Sam Wannan magana ce kawai

APC Basu fita. Kuma kungiya yanzu suka fara. Taskar labarai sunga jagororin kungiyar suna to waya da amsar wayoyin wasu ..da suke son shigowa a cikinta. Suna Fadi masu Rana da wurin cigaba da haduwa.

Taskar labarai ta gano wadannan fusatattu sun yanke shawarar tsayawa cikin APC suyi mata barna.taron da akayi dasu Mai makon ya dinke sai ma ya Kara Rauni.mai zafi…

Da yawa sun fusata yadda suke Jin cewa an Bari sun kashe kudinsu..sannan suka gano an marawa wasu baya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here