JAM IYYAR PRP ZATA YI TARON TA NA KASA A WATAN DISAMBA

0

JAM IYYAR PRP ZATA YI TARON TA NA KASA A WATAN DISAMBA
………ANYI ZABEN SHUGABANNIN PRP NA JAHAR KATSINA

Muazu hassan
@ katsina city news
Sakataren tsare tsare na kasa a jam iyyar PRP Alhaji sule Muhammed kankara ya bayyana a katsina cewa, jam iyyar PRP ta shirya ta tsaf don gudanar da taron ta na kasa a ranar 11 ga watan disamba mai zuwa na 2021.
Sakataren ya bayyana cewa, jam iyyar ta rubuta ma hukumar zaben mai zaman kanta ta kasa.da sauran jami an tsaro da hukumomin da abin ya shafa akan wannan shiri na su.
Alhaji sule Kankara yana magana ne, a taron PRP na jahar katsina Wanda aka yi a ranar asabar 30/10/2021 domin zaben shugabannin jam iyyar na jahar katsina.
Zaben Wanda akayi a garin Dandagoro karamar hukumar batagarawa ya samu halartar manyan yan PRP a katsina.
Cikin su har da farfesa Aliyu jibia. Malami a jami ar Bayero dake Kano.
Da Alhaji Abdurrahman abdallah tsohon shugaban ma aikata na jahar katsina.da malam Abu Aminu yar adua.tsohon mai ba marigayi Umaru Musa yar adua shawara. Da Alhaji Aliyu tsauri.da Alhaji Musa Muhammad kankara.da giggan mutane da suke rike mukamai daban daban a gwamnatocin baya.
Taron anyi shi lafiya tare da sa idanun wakilan hukumar zabe,da na jami an tsaro.da shugaban kungiyar hada kan jam iyyu na jahar katsina. (IPAC)
An zabi mukamai Goma sha shidda inda hassan Hamisu kankara ya zama shugaba na jaha.lawal Muhammad rimaye ya zama sakatare. Sai Aisha indo lawal ta zama shugabar mata.
Duk mukaman Goma sha shidda Goma sha biyu matasa ne yan kasa da shekaru arba in.
Katsina city news
Www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
Www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
Www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here