Jami’an tsaro sun bada belin Ali Baba saboda kalamansa akan Kwankwaso

0

Jami’an tsaro sun bada belin Ali Baba saboda kalamansa akan Kwankwaso

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Jami’an tsaro sun bayar da belin mai bai wa gwamnan kano shawara akan harkokin addinai, Alhaji Ali Baba (a gama lafiya) biyo bayan cafke shi da suka yi saboda wasu kalamai da ya yi game da kamfanin ‘Aliko Oil’.

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta, ta bayyana wa Jaridar Taskar labarai cewa, jami’an tsaro sun ba da belinsa bisa sharadin janye kalaman da ya yi.

Ali Baba ya yi wasu kalamai ne, inda yace gidan Man Aliko da ke Kano da wasu sassa na kasar nan mallakar tsohon gwamnan jihar ne, Rabiu Musa Kwankwaso,

See also  AN SACE WASU MATA TSAFFI A YANKIN BATSARI

Ya yi kalaman ne a wata hira da aka yi da shi a cikin wani shirin na musamman da gidan rediyon Express da ke Kano ya dauki nauyi.

Majiyarmu ta ruwaito cewa Kamfanin na ‘Aliko Oil’ bai yi ammana da kalaman na Ali Baba ba, wanda nan take ya maka shi a kotu domin neman ya bada hujja a kan furucin da ya yi.

Ba tare da bata lokaci ba hadimin Gwamnan ya amince tare da rubuta takardar janye kalaman nasa, kafin daga bisani aka bayar da belinsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here