Jami’iyyar PDP ta kalubalanci Almakura
Daga Zubairu Muhammad
Jami’iyyar adawa ta PDP a Jihar Nasarawa ta kalubalanci Gwamnan Jihar Alhaji Umar Tanko Al-makura saboda da dakatar da wani shirin da ake gabatarwa da harshen Alago a gidan radio da TV ta NBS mallakar Gwamnatin Jihar.
Da yake zantawa da manema Labarai Shugaban Jami’iyyar PDP ta Jihar Nasarawa Hon.Prancic Orogu yace;wannan abinda Gwamnatin Jihar tayi bai daceba saboda da haka yazama wajibi mu kalubalanci rashin adalcin da Gwamnati tayi na hana gabatar da wanan shirin da aka dade ana amfani dashi cikin harshen Alago a wanan kafar yada Labaran.
Hon.Orogu yace; yin haka ya sabawa ka’idojin mulki saboda wanan shirin da ake gabatarwa bai sabawa dokaba kuma sunayine da zimman kiraga alumma domin samun zaman lafiya a tsakanin kabilar Alago da sauran alumma .
Hon. Orogu yace; lokacin da mukaji labarin an dakatar da wanan shirin mun tuntubesu mai ya faru sai akace wai Gwamnati ta dakatarne saboda anayiwa Jami’iyyar PDP kamfen na zave, wai ana hana alumman Alago su zabe Gwamna Al-makura a zave mai zuwa sai dai su zave PDP.
Yace; mun bukaci a bamu kaset na shirin kuma mun saurara bamuji wani batanci ga Gwamnati ba. Sannan bamuji inda sukayi kira da azave PDP ba.
Saboda haka abinda Gwamnati tayi ya sabawa doka koda ba kabilar Alago bane akayiwa haka ,ko Kwaro ko TV ko Gwandara ko Kambari ko Eggon ko Hausawa da kawata kabilar dake zaune a Jihar Nasarawa akayiwa haka dole mufito muyi magana.
Yan qasane kuma yan Jihar ne sunada yancin fadin albarkacin bakinsu.
Hon.Orogu ya kara da cewa ; Gwamna Al-makura yana adawa da kabilar Alago ne saboda yasan bazasu zabe shi a matsayin Sanata ba.saboda babu abinda yayi tsawan shekara shida kan Mulki bai tsinana komaiba masamman a yankin Alago. Duk da dumbin dukiya da ya karba daga Gwamnatin tarayya kimanin naira biliyon 309 a tsawan shekara shida.
Yace; idan aka hada da abinda Gwamana Abdullahi Adamu da Marigayi Ali Akwe Doma suka samu lokacin mulkinsu baikai abinda Al-makura ya samuba .
Yace ; Abdullahi Adamu yayi shekara takwas Ali Akwe yayi shekara hudu amma abinda suka samu biliyon 86. Kuma anaga ayyukan raya qasa da PDP sukayi a Nasarawa.
Yace; meyahana Al-makura ya kashe koda biliyon daya a yankin da kabilar Alago suke dayawa tunda yana bukatar kuri’unsu? Amma ya kashe sama da biliyon goma a kauyen Kwandare .
Yanzu yana amfani da wasu yan tsiraru wai suke nima masa jama’a a yankunan Alago, har ana kokarin shirya masa gangami na niman Sanata. Yace; hakane tunda baka basu sunci ba yanzu dole ka basu kuma kabilar Alago mutanine dake da Ilumi da wayewa sunsan maiyimasu kowaye.
Yace; idan ka hana amfani da shirin da akeyi da harshen Alago saboda kana bukatar kuri’a to ai ba kai kadai bane xan takara,. Mutum uku cikin masu niman kujerar Sanata a yankin Nasarawa ta Kudu duk Alago ne.saboda Yusuf Egebula da Sanata Adekwe da Muhammad Ogoshi Onahu duk Alago ne kai kadaine wanda ba Alago ba.
Sannan ya bukace da ya daina takurawa alumma kosuwaye matukar abinda akeyi bai sabawa doka ba kuma ya sanya a maida shirin da akeyi saboda jama’a suna amfana dashi .