Shahararriyar jarumar nan ta fina-finan Hausa Hajiya Hauwa Maina ta rasu jiya Laraba da daddare.
Rahotanni sun bayyana cewa ta rasu ne a asibitin Malam Aminu Kano bayan ta sha fama da jinya.
Ana sa ran za a yi jana’izarta a yau Alhamis a garin Kaduna, inda take zaune gabanin rasuwarta.
Hauwa Maina na daga cikin matan da suka jima suna fitowa a fina-finan Hausa.
Tun 1999 ta fara fim din Hausa, bayan ta koma garin Kaduna da zama.