JAWABI KAN CI GABA DA AKA SAMU A AYYUKAN OPERATION SAHEL SANITY DAGA 1 YULI – 4 SATUMBA 2020
Daga yayin kaddamar da atasayen Soja da akeyiwa lakani da Operation SAHEL SANITY a wani bangare na bukukuwan shekera na tunawa da ranar Sojojin Kasa na Najeriya wanda aka gudanar a Babban Sansanin Soja na musamman a garin Faskari ta Jihar Katsina, babu shakka wannan atasayen ya kawo alfanu ga rayuwar yau da kullum ta mutanen wannan yanki na Arewa maso Yamma baki daya. Zaa iya tunawa an kaddamar da atasayen ne domin tallafawa rundunar Operation HADARIN DAJI domin kawarda ayyukan miyagu irin su yan bindiga dadi, masu garkuwa da mutane, masu satar dabbobi, yawan kashe kashe da makamantansu. Babu shakka an samu raguwar waddannan miyagun ayyuka sakamakon kokarin Sojojin Operation SAHEL SANITY da jajircewarsu ba dare ba rana inda wannan ya jawo dawowar harkokin noma, kasuwanci da ma’amalolin yau da kullun cikin kwanciyar hankali da nishadi.
An tabbatar da wannan bisashe yayin ziyarce ziyarcen da Ciyamomin Kwamiti kan harkokin Sojan kasa na majisar tarayya gami da Gwamnoni da ma manyam Sarakunan wannan yanki suka kawo Shalkwatar wannan Sansani na Operation SAHEL SANITY a nan garin Faskari, Jihar Katsina daga ranar 7 – 14 August 2020. Dukkanin manyan bakin, sun yaba da kokarin Jamian Sojan wajen ganin yadda suke kawar da ayyukan laifuffuka daga wannan yanki baki daya. Haka zalika, sun shaida da yadda ayyukan noma, kasuwanci da hada – hadar jamaa cikin kwanciyar hankali suke dada habaka ba tare da tsangwama ko musgunawa ba.
Wadannan dunbin nasarori da aka cimma daga fara wannan atasaye na nuni ga sadaukar da kai, bajimta da kishin kasa na Sojojin Operation SAHEL SANITY inda abin takaici wasunsu suka rigamu gidan gaskiya wajen ganin sun kara rayukan mutune da dukiyoyin alummar wannan yanki.
A tsakanin wannan lokaci, zaratan Sojojin Operation SAHEL SANITY sun gudanar da sharar maboyar yan bindiga dadi, kwantan bauna da sunturi domin hana miyagu damar cutar da mutane. Haka zalika sun gudanar da sintiri a gonakai domin kare manoma a Jihohin Sokoto, Katsina, Kaduna, Kebbi da Zamfara inda yin hakan ya bunkasa ayyunkan noma da karawa manoman yankin kwarin gwiwa.
Mafi mahimmancin wannan atasaye shine nasarar kubutar da wadanda akayi garkuwa dasu, da kwato shanun sata, gami da kame yan bindiga dadi da masu tallafa masu, gami da cafke masu safarar miyagun makamai na gida da na ketare da kuma wargaza gungun masu hakar maadanai na haram. Haka nan kuma, rundunar tayi nasarar kama dumbin makamai da alburusai da babura gami da toshe hanyoyin da yan bindiga dadi ke samum tallafi. Kawo yanzu, a jimlar atasayen da ya gudana, dakarun sunyi nasarar kakkabe yan bindiga dadi 100, sun kuma kwato shanun sata 3,984, kananan dabbobi 1,627 gami da rakuma 3. Haka kuma dakarun sun damke yan bindiga dadi 148 da kuma barayin ma’adanai 315. Bugu da kari, an kame dunbin makamai wanda suka hada da bindiga kirar AK 47 – 43, bindiga mai jigida kirar GPMG -1 da bindigogi kirar gida- 100, gami da harsasai na bindigar AK 47 guda 3,261 da harsasan indigo kirar gida – 151.
Haka kuma, dakarun sunyi nasarar ceto mutane 107 da akayi garkuwa dasu game da cafke masu baiwa yan bindiga dadi bayanai guda 20, masu safarar miyangun makamai – 6, masu cinikin dabbobin sata – 13 da masu safarar kayan masarufi zuwa wajen yan bindiga dadi – 32. Bugu da kari, an rugurguza maboyar yan bindiga dadi – 81 cikinsu harda zangon fitinannen dan bindiga dadi da ake kira da suna DANGOTE.
A wani bangare, dakarun sun yi nasarar kawar da farmakin yan bindiga dadi kan jama’a har guda 74 da kuma farmakin masu garkuwa da mutane har guda 54. Dakarun Operation SAHEL SANITY na ci gaba da ayyukan su wajen gudanar da suntiri, da fatattakar miyagun masu laifi domin ganin jama’a sun ci gaba da walwala.
A sakamakon haka, ana yabawa Sojojin domin sadaukar da kawunan su gami da nasarorin da aka samu cikin wannan karamin lokaci. Haka kuma an bukace su da su kara kaimi wajen cimma Karin nasarorin a nan gaba. Bugu da kari, an bukaci jama’a da suci gaba da baiwa Sojojin hadin kai da bayanai kan ayyukan yan ta’adda domin kawo karshen su baki daya. Hukumar Sojan kasa ta Najeriya na tabbatarwa da jama’ar yankin Arewa maso Yamma da matsayinta kan kawar da duk wani yanayi da zai kawo nakasu ga rayuwarsu.
Mun gode.
AMINU ILIYASU
Colonel
Nigerian Army Operations Media Coordinator
5 September 2020