Jerin Tallafin ‘Future Assured’ a Kano

0

A watan Mayu na wannan shekarar na rubuta Makala akan yadda matar Shugaban Kasa Hajiya Aisha Buhari ta zama jagora wajen bayar da tallafin na annobar COVID-19 a Kano. Da farko na yi ta ne da harshen turanci sannan na fassarata aka buga a Jaridar Hausa Leadership ta ranar Laraba 20 ga watan Mayu, 2020, sannan na saka a kafofin sadarwa na zamani irinsu Facebook da sauransu. A ciki na kawo sunayen muhimman kungiyoyi da hukumomin da suka yi namijin kokarin wajen tallafawa alummar kano irin su Future Assured Foundation ta Hajiya Aisha Buhari, BUA Foundation, Gwamnatin Jihar Kano da Dangote Foundation.

Daga wannan lokaci ban yi kasa a guiwa ba wajen bin diddigin wannan tallafi da wadannan gidauniyoyi da hukumomi suke bayarwa ga talakawan Jihar Kano domin

rage radadin da annobar ta COVID-19 ta kawo. A wannan gabar ne zan jinjinawa Future Assured Foundation saboda namijin kokarin da ta yiwa mutanen Kano kasancewar ta gidauniya guda daya tilo daga wajen Kano da ta dau tsahon wata shida ta na kawo tallafi ba tare da hutu ko gajiyawa ba, baya ga sauran Jihohi da Suma take kai musu wannan tallafi na kayayyaki irinsu kayan abinci, magunguna,

kayan aikin įinya, kayan noma da injinan noman rani da sauransu.

Ga jerin tallafin da future Assured Foundation ta ringa yi a Kano, tsahon watanni shida daga watan Mayu zuwa October:

Mayu

Awatan Mayu kayan tallafin na matar shugaban kasa an fara rabasu ne ga wasu kungiyoyi masu zaman kansu, sannan kuma an bawa wasu hukumomi wadanda suke hulda da al’ummomi daban-daban irinsu Hisba, Yan wasan Kwaikwayo, Karota da sauransu.

Wadannan kungiyoyi masu zaman kansu sunyi kokari wajen rarraba kayan tallafin ta yin amfani da hanyar bi gida gida, unguwa unguwa wanda hakan ya yi matukar amfani don alummomi da yawa tallafin ya isa zuwa garesu.

Tallafin na matar shugaban kasa bai tsaya kadai iya kungiyoyi ba har malaman addini da limamai tare da mabiyansu ba a barsu a baya ba.

Yuni

A wata Yuni tallafin na matar shugaban kasa bai tsaya ba an cigaba domin kuwa jirgin tallafin ya cigaba da motsawa musamman tare da kungiyoyi masu zaman kansu da suke Kano irinsu Creative Needy Foundation karkashin jagorancin Fauziyya D Sulaiman, Todays Life Foundation wanda Mansura Isa take jagoranta, da Daso Entertainment ta Hajiya Saratu Gidado wadannan su ne kadan daga cikin wadanda muka iya tattaro bayanansu zuwa yanzu.

See also  Shugaba Buhari Ya Karrama Sarkin Gombe Da Lambar Girmamawa Ta Kasa

Juli

A watan Juli tallafin ya cigaba da tafiya inda aka bawa wasu asibitoci magunguna da gadajen kwanciya da sauran kayayyakin kariya daga kamuwa da cututtuka kamar su COVID19. Jirgin tallafin bai tsaya iya Kano ba ya tsallaka har zuwa sauran jihohin Nijeriya.

Agusta

A watan Agusta ma gidauniyar Future Assured ta Hajiya Aisha Buhari ta yi matukar kokari wajen rarrabawa alummar Kano da ligawa kayan noma da injinan ban ruwa domin noman rani. Haka kuma a cikin watanne gidauniyar ta ga dacewa wajen tallafawa gidajen marayu da gajiyayu tabasu kayayyakin tallafin da suka hada da taliyar yan yara da shinkafa da sukari da madara da tumaturin gwangwani da sauran kayan masarufi na amfanin yau da kullin.

Satumba

A watan Satumba jirgin tallafin na matar shugaban kasa ya cigaba da gudana inda aka kara bayar da kayan tallafin ga Jihar Kano na tabbata da cewar tallafin ya kai ga wadana tallafin ya dace ya kai. Hakan na faruwa ne ta hanyar dagewa da wakilan matan shugaban kasar keyi na ganin amanar da aka basu ya isa ga wadanda a dace.

Octoba

A watan Octoba ma jirgin tallafin ya isa ga marayu da marasa gata da ke cikin birnin Kano. A wannan gabar ne gidauniyar Creative Needy Foundation ta mayar da akalar tallafin zuwa ga zawarawa da iyayen marayu.

Wadannan su ne daki daki yanda aka gudanar da rarraba kayan tallafin na matar shugaban kasa wanda a karan kai na nayi kokarin harhada bayanai da na samu da kuma hotuna da jawabai da suka nuna yadda aka bayar da tallafin bisa tsari.

Amma na tabbar da cewa su gidauniyar Future Assured suna da bayanan tallafin da suka fi wannan saboda su ne suke aiwatar da tallafin. Haka nan kuma wannan rahoto da nayi kokari na tattarasu iya Kano ne Jiha ta inda nafi wayo banda sauran jihohi wanda su ma na tabbatar an yi abin da akayi. Abin sha awa shi ne tunda cutar Covid 19 ta shigo matar shugaban kasar ba ta hutaba kullin yi ake yi ba tare da gajiyawa ba.

Ina fata wannan rubutun zai zama silar shigar wasu masu bada irin wannan tallafin wajen yin koyi da yanda uwargidan shugaban kasar ta ke raba nata tallafin, don yin koyi da ita din abu ne mai mutukar muhimmanci ga al’ummarmu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here