JIRGI YA KASA TASHI SABODA MATSALA

0

JIRGI YA KASA TASHI SABODA MATSALA

Daga bashir suleman

Hajjin Bana 2018 Katsina.

A safiyar yau Alhamis 9/8/2018 da misalin ƙarfe 8:01 jirgin Max Air ya sauka a filin saukar jirage na ƙasa da ƙasa na Umaru Musa Ƴar’adua dake Katsina. Domin yin sawu na huɗu a cigaba da ɗaukar mahajjatan jahar Katsina.

Mahajjatan da suka fito daga ƙananan hukomomin Kaita, Jibia, Rimi da sauransu sun kwana a filin jirgin suna jiran isowarsa, wasun an kammala tantancensu har sun hau layi, wasu ma har sun shiga sun zauna.

Sai aka samu bayani daga jam’ian jirgin cewar jirgin yana da ƴar matsala ta ɗigar mai.

A sakamakon tattaunawa da matuƙa jirgin da kuma hukumar jindaɗi da walwala ta jahar Katsina, sai aka cimma matsayar a saukar da mahajjatan, jirgin ya koma Kano dan gyara.

See also  Dogara Yaro ne Sarkin Hausawan Legas - Tinubu

A bisa ga haka ne hukumar jindaɗi da walwalar Alhazan, suka kwantar da hankalin mahajjanta da kuma cigaba da zama tare da su, har lokacin da wani jirgi zai zo.

Mahajjanta sun aminta da gamsasshen bayanin da hukumar Alhazan ta yi masu, sun kuma yaba wa matuƙa jirgin da mahukunta hukumar Alhazai kan yadda suke tafiyar da ayyukansu cikin kwanciyar hankali da lumana.

Saboda nuna kulawarsa ga al’umma da yadda yake hidima kan ganin komai ya tafi dai dai, Amirul Hajj na jaha kuma kakakin majalissar dokoki na jahar Katsina, Rt Hon. Abubakar Yahaya Kusada cikin hanzari ya iso farfajiyar saukar jiragen dan ƙara kwantar da hankalin Mahajjatan, da kuma cigaba da zama tare da su dan cigaba da jiran zuwan wani jirgin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here