Jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja ‘ya taka nakiya an kuma buɗe masa wuta’
An kai wa wani jirgin ƙasa da ya tashi daga Kaduna zuwa Abuja babban birnin Najeriya hare-hare har biyu, kamar yadda wani tsohon Sanata daga jihar Kaduna Shehu Sani ya ce.
Sanata Shehu Sani ya wallafa a shafinsa na Tuwita a ranar Alhamis da safe cewa an kai hari kan jirgin yamma na ranar Laraba inda jirgin ya taka nakiya, sannan aka buɗe masa wuta a daidai saitin da direba yake da kuma tankin jirgin.
Ya kuma ƙara da cewa an sake kai hari kan wani jirgin na safiyar Alhamis da shi sanatan ke ciki inda ya taka nakiya ta fashe har ta lalata hanyar jirgin.
“Ina cikin jirgin da safiyar nan a lokacin da jirginmu ya bi ta kan nakiya ta tashi.
“Ikon Allah ne kawai ya sa muka tsira,” kamar yadda Sanata Sani ya wallafa
Rahoto: Comrade Musa Garba Augie.