KA GINA MA JAMA A TA RIJIYAR BURTSATSE

0

KA GINA MA JAMA A TA RIJIYAR BURTSATSE
….inji Musa usman
Wani mai gadin wani kamfanin indiyawa.mai suna Musa usman.ya ba shugaban kamfaninsa da yayi shekaru ashirin da biyar yana gadi mamaki.
Musa ya kwashe wadannan shekaru yana aiki.cikin gaskiya da rikon amana mai kamfanin ya gama aikinsa a Najeriya zai koma gida, sai gina ma yaron sa gida ginannen kuma ya Sanya duk kayan alatu.yace ya bashi kyauta.
Musa Usman wanda ya fito daga kauyen giljimmi .karamar hukumar birniwa ta jahar jigawa.
Sai ya ce ma ubangidan nasa shi yafi bukatar a bar gidan ya rike abinsa.amma yaje kauyen su ya Gina masu rijiyar burtsatse.saboda yasan yadda mutanensa ke wahala akan ruwan sha
Ba indiyen mai suna Mr v verghasa.sai amsa masa yaje kauyen ya Gina masu rijiyar burtsatse.a ranar kaddamar da ita kuma yace ya bar masa gidan da ya Gina masa.yace mai gadin nasa,mutum ne mai gaskiya da amana.don haka yayi masa wannan kyautar

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here