Kabilar da suke bewa ungulu gawar yan uwansu idan sun mutu memakon su binne gawar

0

Al’ada wata aba ce da kabilu da yawa suka dauke ta da mahimmanci wasu ma kamar addini haka suka mayar da abin…

 

Kusan kowacce kabila suna da al’adar da suke gabatarwa wanda suka taso suna yi tun iyaye da kakanni, wasu al’adun gwanin birgewa wasu kuma sai a hankali domin abinda suke gabatarwa cikin kabilar tasu a matsayin al’ada kwata kwata sai a hankali.

 

Da dai sauran abubuwa, to yau cikin shirin namu zamu kawo muku wata kabila ce da idan dan uwansu ya mutu basa binne shi saidai su kaiwa ungulaye (vultures) su cinye gawar.

 

Kamar yadda kowa dai ya riga ya sani a addinai guda biyu da muke dashi musulunci da kuma addinin kirista duk wani mutum daya mutu binne gawarsa ake.

 

To saidai su a wannan kabilar ta Tibetan sky cikin addinin Buddhism ko kuma muce addinin Budda su idan dan uwansu ya mutu basa binne shi saidai su samu wani farin kyalle su rufe gawar su dauke ta su kaita can kwanar kofar gidan su ajiye zuwa kwana uku ko kwana biyar

See also  Juyin Mulki: Takunkumin ECOWAS ya fara aiki a Nijar, an datse wutar lantarki a kasar

 

Dangin wanda ya mutum sukan daina aikata komai saidai su share ko ina su tabbatar babu datti a gurin wai domin ruhin mamacin ya samu gurin zama mai kyau.

 

 

Iyalan mamacin bayan sunyi hakan sai su zabi rana daya wacce suke ganin tafi sauran ranakun daraja sai su dauke wannan mamacin su kaishi can wani guri kusan wasu duwatsu sai su zaunar da gawar su dora kan gawar bisa gwiwarsa.

 

 

Daga nan sai su tafi su barwa ungulun da suke gurin su zo su cinye naman gawar.

 

Daga zarar sun cinye shekenan sai yan uwan mamacin su tafi suna farin ciki wai dan uwansu ya tafi babu wani zunubi a kansa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here