TUNA BAYA: KANTIN LITATTAFAI NA ‘ILMI’ KATSINA
@Taskar Labarai
A tsakanin shekarun 1975 zuwa 1989 a garin Katsina an yi wani shahararren kantin sayar da littattafai, mai suna ‘Ilmi’ Education Supply Company.
Kantin yana a bayan gidan waya na jihar Katsina. A lokacin kantin shi ne kadai dila na littattafai na kamfanin buga littattafai na NNPC dake Zariya.
Ana tallar kantin a gidan rediyon jiha, da kuma NTA Kaduna, shi ne ke kai littattafai duk makarantu dake fadin yankin Katsina.
Alhaji Ammani Bookshop shi ne ke da shagon, yana da yara masu tsaro da kuma masu kai littattafai a makarantu a wata mota fijo a kori kura.
Wannan hoton na sama yanzu yadda shagon ya koma, gidan da shagon yayi ta shiga hannaye, yanzu wakilin Katsina Alhaji Kabir Murnai shi ne ya mallake shi.
Allah yayi wa Alhaji Ammani Bookshop rasuwa a karshen shekarun 1990, ya bar ‘ya:ya da jikoki da daman gaske, daga cikin ‘ya’yansa akwai daya da ya koma Pasto bayan ya auri wata malamar addinin kirista a garin Jos.
Marigayi Alhaji Ammani Bookshop mutumin kirki ne, mai taimakon na kasa da shi, har ya rasu yana sana’ar ta sayar da littafi.
Duk ‘ya’yanshi ko jikoki babu wanda ya gaje shi, tarihin Katsina ba zai manta da shi ba, akan yadda ya bada tasa gudummuwar ta habaka ilmi a Katsina. A bangaren sayar da littattafai.