inji Tsohon sarkin Kano
Daga Ibrahim Hamisu, Kano
Tsohon sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, ya ce abin da gwamnatin tarayya ta yi wajen farfado da tattalin arzikin kasa ya yi daidai.
A karshen makon nan ne aka rawaito tsohon sarkin ya na cewa tun kafin a gamu da annobar COVID-19, ya kamata gwamnati ta dauki wadannan matakai.
A wata hira da akai da shi a gidan talabijin din Arise TV a ranar Juma’a, 4 ga watan Satumba, Sanusi II ya ce cire tallafin man fetur da aka yi, shi ne abin da ya dace.
“Wadansu matakai da ake dauka kwanan nan, wadanda aka aro daga IMF na cire tallafin man fetur, duk da zafin yin hakan, su ne abubuwan da su ka dace ayi idan ana so kudin asusun gwamnati su karu.”
Sanusi II ya kara da cewa: “Yanzu an samu karuwar gaskiya a hukumar NNPC.”
“Na ji cewa NNPC ta zuba kusan Naira tiriliyan biyu a asusun FAAC, wanda wannan ya fi abin da aka tara a tsawon shekaru.”
Tsohon sarki ya kara da cewa idan aka samu gaskiya wajen sha’anin mai, za a ga canji a sauran bangarorin gwamnati.
Sai dai duk da nuna goyon baya da tsohon gwamnan na CBN ya bada na zare tallafin mai, ya ce akwai gyara a lamarin yadda kasar ta ke kashe kudi.
“Gwamnati ta duba yadda ta ke batar da kudi, ta tabbatar cewa ya na kai wa ga talakawan kasa.”
A cewarsa, ya kamata gwamnatin tarayya ta rika kashe kudi ne a harkar ilmi, ruwan sha, cigaban karkara, ya ce wannan ya fi muhimmanci a kan gina gidaje da gada.