KASAR NAN BA TA GA CANJI NA ALHERI BA
Sanata Mamman Abubakar Dan Musa
Daga Danjuma Katsina.
Daya daga cikin dattawan Katsina masu mutunci Alhaji Mamman Abubakar Dan Musa, wanda yake tsohon sanata ne kuma tsohon kakakin majalisa a tsohuwar jahar Kaduna. Kuma gogaggen lauya ya ce; “Sam kasar nan ba ta ga wani canji na Alheri ba a hawan jam’iyar APC bisa jagorancin Muhammadu Buhari a shugaban kasa”.
Dan Musa ya bayyana haka ne a taron manema labarai da aka yi a dakin taro na gidan Abba Saude a Katsina.
Sanatan ya ce lokacin shiru ya kare dole ne dattawa irinsu, su fito su yi magana. Ya kara da cewa, “Tsaron da ake maganar an samu, a kwanan nan gwabnan Katsina sunkutukum ya fito ya ce masu satar mutane da barayin daji sun ma jahar ta Katsina kawanya. A jawabin na gwabna ya ce hatta shi kansa bai tsira ba. Sa’annan kuma kwanan nan ne aka tare Galadiman Katsina hakimin Malumfashi, aka tafi da mai masa hidima.
Sanata Mamman ya ce garinsu na Dan Musa ya zama kullum waje ne na hari da sata, wanda ta kai dole ne sai da jama’a suka hada kansu don kare kansu daga hare-haren mabarnata.
Kasuwar Dan-Musa wadda tana daya daga cikin kasuwanni mafi girma a Katsina yanzu ta zama kufai, an kaurace mata saboda tsoron yan fashi da masu satar mutane. Dan-musa ya kara da cewa saboda wannan ta’annati, yanzu matasanmu sun zama yan gudun hijira a garuruwan kudancin kasar nan na jihohin Benin, da Lagos, da Osun sun bar gonakinsu da barayin shanu suka hana su nomawa, sun koma Kudu da kuma Yammacin kasar nan neman abinci.
Dan-musa ya ci gaba da cew ya za ka ce mu yi shiru, wannan bala’in da ya shafe mu? Kalli abin da ke faruwa a jahar Zamfara makwabciyar jaharmu, da kuma abin da ke faruwa a kananan hukumomin Jibiya, da Batsari, da Safana, da Dan-musa, da Kankara, da Faskari, da Dandume, da kuma Sabuwa na kisa da satar mutane. Kuma har yanzu an ki fada wa jama’a cewa ga mafita.
Sai Dan-musa yace; “Ranar asabar mai zuwa za a yi zaben shugaban kasa, kuma ni Mamman Abubakar Dan Musa na yi wa Muhammadu Buhari, kamfen a shekarun 2007, 2011.da 2015, amma gaskiyar magana bayan zaben na Buhari a matsayin shugaban kasa ba a abin da na gani a yankina, sai rashin tsaro mafi muni. Kuma tsaron da ake magana an samu an mai da hankali ne kawai a jahohin Arewa maso Yamma. Watau tsohuwar jahar barno. Amma mu a jahohinmu inda shugaban kasa ya fito, yanzu muke a cikin tashin hankali.”
Dan-musa ya ce hatta nasarar da ake ikirarin an samu na tallafa wa manoma, tatsuniya ce kawai, duk mai so kuma ya je ya tambayi manoman Jibia, da Batsari, da Safana ko Dan-musa za su fada masa gaskiyar halin da suke ciki.
Dan-musa, ya ce a kan karyar an farfado da masana’antu, duk katsina a fada mana masana’anta daya da aka farfado da ita, wadda matasanmu suka samu aikin yi a cikinta? Amma a kudancin kasar nan irin su jahohin Ogun, da Abia, duk sun ga hakan. Kuma masana’antunsu, na ta daukar matasansu aiki.
Maganar yaki da cin hanci da rashawa kuwa ya ce, yaki ne kawai wanda yake kamawa da hukunta duk wadanda aka dauka a matsayin makiyan gwabnatin dake bisa mulki.
Da farko gwabnatin ta sama ta ce, za ta bayyana sunayen wadanda ake tuhuma da kaddarar da aka kwace a wajensu, amma har yanzu saura kwanakin zabe Kazan, amma ba su yi hakan ba. Kuma kwanan nan kungiyar dake sa ido ga kasashe a kan cin hanci a duniya (TIN ), ta ce yakin da Najeriya ke yi da cin hanci takaitacce ne.
Dan-musa ya kara da ce wa, masu rike da mulkin nan su sani, yadda yanzu su ke tuhumar wadansu haka wata rana za ta zo a kansu, don an yi irin haka a kasashen kudancin Koriya da Birazil. A kasar birazil, tsaffin shugabanin kasar biyu a ka kama da laifi, kuma yanzu haka duk suna a gidan yari.
A kasar Koriya kuwa tsohon shugaban da abokan kasuwancinsa, duk suna gidan yari. In lokacin yazo komai tsufan mutum sai ya fuskanci hukunci, don hakan ta faru ga shugabanni kamar Ruz a kasar Kambodiya.