KATSINA 2023 TARIHIN FAROUK LAWAL JOBE.

0

KATSINA 2023
TARIHIN FAROUK LAWAL JOBE.

Bishir Suleiman
@Katsina City news

Dakatar a irin wannan lokaci na bukatar masani musamman wanda ya gwanance wajen sanin hada-hadar kudi da mu’amula da jama’a, ta yadda za bunkasa tattalin arzikinsu da kuma sa ma masu kyawawan hanyoyin inganta rayuwa.

In har aka dubi matakai na ilmi na Faruk Jobe, aka zabe Shi sabon Gwamna Katsina. Za a san an ba, jagoran da zai kyautata rayuwar al’umma duba da matakan ilmomin da ke gare shi.
karatun farko da aka bude kwakware jobe dashi shine .karatun addinin musulunci Wanda ya fara da sanin bakaken Akur ani mai tsarki da na litattafan koyon ibada da tarbiyar irin ta musulunci.
Ya fara ilimin zamani da firamare ta garinsu, wato Kankara Primary School a shekarar 1973 zuwa 1978, sannan ya tafi Teachers College, Dutsin-ma a shekarar 1978 – 1983 bayan ya kamala, ya tafi College of Education, Kafancan a shekarar 1983 – 1986. A kuma shekarar 1988 ya shiga jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, inda ya gama a shekarar 1990 daga bisani kuma ya tafi jami’ar Maiduguri a shekarar 1995 – 1996 sanna ya samu halartar jami’ar Danfodiyo Sokoto a shekarar 1998 – 2000

See also  Kungiyar ALGON Reshen Jihar Katsina Ta Rubuta Takardar Koke Zuwa Ga Ministan Shari'a

Wadannan Makarantu da ya halarta, ya ba shi damar mallakar shaidar karatu kamar haka:

– Satifiket na Kammala Firamare a shekarar 1978
– Satifiket na Shaidar Malanta Grade II a shekarar 1983
– Satifiket na Malanta NCE a shekarar 1986

– Digiri kan ilmin Nazarin halayyar Dan’adam ( B.Ed Social Studies) a shekarar 1990

– Digirin Kwarewa kan Tsarin tafiyar al’umma ( MPA) a shekarar 1996

– Digirin Kwarewa kan Tsarin Harkokin Kasuwanci ( MBA) a shekarar 2000

Duk da haka Dantakarar yana da Shaidar kwarewa a ta HCIB wato Honorary Permanent Senior Member, of the Chartered Institute of Bankers of Nigeria. Da kuma CCrFA wato Member, Chartered Certified Forensic Fraud Examiners of Nigeria.

Wannna ne ya kai shi ga tushen samun nasara a kan ayyukan da ya gudanar, da kuma tabbatuwarsa cikakken mutum Wanda ya dace da zama sabon angon Gwamnatin Katsina.

Zamu dora a biyo mu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here