KATSINA, MA’AIKATA, ALBASHI DA CIWO BASHI

0

KATSINA, MA’AIKATA, ALBASHI DA CIWO BASHI…………

Mu’azu Hassan

@Katsina City News

Jihar Katsina na daya daga cikin Jihohi masu yawan mutane a Nijeriya. Tana da yawan jama’a kusan miliyan 10.

Tana daga cikin Jihohi da suka fi yawan ma’aikatan gwamnatin Jiha da na Kananan Hukumomi.

Jihar tana da tarnaki da matsaloli masu yawa. Masu mulkinta sun samu wasu nasarori, sun kuma yi kurakurai.

Duk da halin da tattalin arzikin duniya ya shiga, wanda kuma ya shafi Nijeriya sosai, ya kuma taba duk Jihohi har da Katsina, akwai inda Jihar ta yi zarra, kuma ta zarce tsara a kasar nan.

Wannan kuma jajircewa ce ta masu mulki da kin koyi da wasu Jihohin. Sun yi abin da suke ganin shi ne ya yi masu daidai.

A Jihar Kaduna, Gwamnan na hawa a 2015 ya kafa kwamitin da za a ga bayan ma’aikatan Jihar. Kwamitin da rahotonsa ya kai ga sallamar sama da ma’aikata dubu 30, a Jihar kuma har yanzu ba a gama ba.

Kaduna ta ciwo bashin da har ta kure cin bashi, kamar yadda Hukumar da ke kula da cin bashin Jihohi suka tabbatar. Kaduna na cikin Jihohin da aka haramtawa cin bashi, don ta ci har iya wuya.

Kaduna ga korar ma’aikata, ga cin bashi, duk da kuwa albashinsu bai kai na Jihar Katsina ba.

A Jihar Kogi, su albashi sai abin da ka gani a lokacin da ya iso. Kamar yadda ma’aikatan Jihar suka tabbatar mana, suna bin watanni, kuma babu ranar biya. Wayon da Gwamnan ya yi shi ne, kullum kwamitoci ke aiki a kan albashin ma’aikata. Da wannan ake fakewa, sai an gama aiki za a fara biya a kan lokaci. Shi ma ya dakatar da dubban ma’aikata sai an gama bincike. Wani lokaci a Jihar sai a yi ‘bonanza’, a ce ga dan wani abu ga kowa cikin albashi kafin a gama bincike.

Wasu Jihohin suna biya, amma yawan albashin bai kai ko kusa da na Katsina ba, kuma ba su da yawan ma’aikata kamar Katsina. Misali a Zamfara, mai Digirin farko a Jiha dubu 30 yake dauka. A Karamar Hukuma dubu 20 da doriya, mai Sakadandire dubu shida.

Wata Jihar wadda ke tsare albashi ita ce Jihar Jigawa, yawanta da ma’aikatanta bai kai na Katsina ba, amma a bincikenmu albashinta yana daidai da tsarin mafi karancin albashi na kasa.

A wasu Jihohin tuni suka bar daukar mai Sakandire aiki da Diploma. Misali a Jihar Kano, in kana da karatun Sakandire kar ka je neman aiki. In kana da Diploma kar ka je nemin aikin dindindin a gwamnatin Jiha, sai dai na wucin-gadi (casual) ne.

Akan dauki masu Diploma da NCE a sashen koyarwa.

A wannan binciken mun tattara duk albashin Jihohin kasar nan don wannan rubutun, wanda yana da sauki da wahala ga duk mai bukatar tabbatarwa.

See also  DAN TAKARAR GWAMNA ZAI CIWO BASHI MAI TSADA

Mun ba da misali da Jiha hudu ne kawai a matsayin misali.

Da yawan Jihohi sun manta da wani abu wai shi karin girma ga ma’aikaci don kar kudinsu su karu. Kullum za a yi ta kafa kwamitin daukar lokacin da janye tunani. A ce sai ya gama aiki za a yi karin girma. Wasu ma sun fito karara sun ce ba su da kudi, ba sauran karin girma, sai Baba ta gani.

A Katsina, har yanzu ana daukar masu Sakandare da matakin albashi mafi karanci. Jihohi da yawa sun bari.

A Katsina har yanzu ana karin girma a kai, a kai, wanda Jihohi da yawa sun bari.

A Katsina ba a kori ma’aikata ba, kuma ba a kafa kwamitin wasa da hankali ba. Jihohi da yawa suna cikin wannan taskun.

A Katsina suna bin matakin albashi mafi karanci kamar yadda dokar kasa ta ce. Jihohi da yawa sun ki biya, wasu sun fara suka ce sun jinjigine.

A Katsina ana biyan albashi kafin a shiga makon wani sabon watan. Jihohi da yawa sai abin da suka gani.

A wannan yanayi yana da kyau ma’aikatan Katsina su gode wa Allah da ya tsare masu aikinsu da albashinsu, ya zama ba a samu matsala irin ta wasu Jihohin ba.

A bangaren bashi kuwa, duk wanda ya nemi bayani a ofishin Hukumar da ke kula da bai wa Jihohin kasar nan bashi da ake kira DMO, zai ga bashin da ake bin kowace Jihar. Za ka rubuta ne ka bi har a ba ka amsa. Neman bayani a kan yadda mutum zai amshi bashin kyauta ne, ko Sisi ba ka biya.

Zai ga cewa yanzu Jihohin kasar nan hudu ne kacal ba su ci bashi har iya wuya ba. Katsina ce ta farko.

Da yawan Jihohi an riga an shafa masu bakin fenti kar a kara ba su bashi.

In mai bincike ya tambaya zai ga cewa duk bashin da Katsina ta ciwo basussuka ne na inna-rididi, kuma wasu na Bankunan Musulunci ne marasa wani hatsari a gaba.

Wasu Jihohin ana fargabar duk wanda ya hau hayaniyar biyan bashi ta ishe shi. Ya zuwa yanzu Jihar Katsina ba ta cikin wannan fargabar.

Duk wanda zai zo fargabarsa ita ce, ma’aikata, kudin shiga da kuma albashi.

Bincikenmu ya tabbatar cewa da Katsina na kan gaba a kasar nan wajen rike albashin ma’aikata, karin girma kiyaye dokar mafi karancin albashi da daukar kananan ma’aikata a cikin aikinta.

Kuma tana cikin Jihohin kasar nan hudu da ba su ci bashi ya sarke su ba. Ya dace ma’aikata su gode wa Allah a kan haka.

Wannan binciken da hadin gwiwar Matasa Media Links Ltd aka yi shi, don jaridun

Katsina City News.

@www.katsinacitynews.com

Jaridar Taskar Labarai

www.jaridartaskarlabarai.com

The Links News

@ www.thelinksnews.com

07043777779.08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here