Kiran Kungiyar Arewa Media Writers zuwa ga Gwamnonin Arewa

0

Kiran Kungiyar Arewa Media Writers zuwa ga Gwamnonin Arewa

Kungiyar “Arewa Media Writers” ta na kira ga gwamnatin Nijeriya da Gwamnonin Jihohin yankin Arewa dasu gaggauta kawo karshen ta’addacin dake faruwa a Jihohin su, domin yankinmu na Arewa ya zauna lafiya.

Daga Abdulhakim Muktar

Cikin mako guda ‘yan bindiga sun kashe kimamin mutanen da ba zasu kirgu ba, a Jihohin yankinmu na Arewa, tare da garkuwa da mutane masu yawa da zummar karbar kudin fansa.

Wannan ta’addacin da ‘yan ta’addan suke yiwa al’ummar yankin mu ya shafi jihohi da dama a yankunan Arewa, da suka hada da Jihar Kaduna, Zamfara, Katsina, Sokoto, da wasu daidaikun Jihohin ga ta’addacin Boko Haram da yaki ci yaki cinyewa a yankin Arewa maso gabas.

Ta’addacin da ake yiwa al’ummar yankin Arewa a wa yan nan Jihohin yayi matukar muni, ana binsu har gida ana kashe wa tare da kona wasu da ransu, ana kone dukiyoyin su ba suji ba, basu gani ba, a wasu yankunanan jihar Zamfara an hana wasu kauyuka da yawa zuwa gonakinsu matukar basu biya yan ta’ddan wasu kudaden da suka nema ba.

See also  Rikicin Jagorancin Sallah Ya Shafi Sallar Juma'a a wani Masallaci dake Kano

Haka zalika masu garkuwa da mutane don biyan kudin fansa sun addabi hanyar Abuja zuwa Kaduna da wasu Jihohi, wanda a ranar Litinin da ta gabata sun kama dalibai masu yawa, inda suka nemi kudin fansa kimamin kudin da yakai miliyan 270.

Da wannan ne Kungiyar marubutan Arewa a kafofin sadarwar zamani, “Arewa Media Writers” karkashin jagorancin shugaban kungiyar na kasa Comr Abba Sani Pantami, take kira ga gwamnatin Nijeriya da gwamnonin Jihohin yankin Arewa, dasu gaggauta kawo karshen ta’addacin dake faruwa a Jihohin su, don al’ummar yankin mu na Arewa su zauna lafiya.

Fatan kungiyar “Arewa Media Writers” har kullum shine Allah ya kawo wa yankin mu na Arewa zaman lafiya mai dorewa. Amin

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here