KO ANYI AMFANI DA KAMFANIN A A RANO AN SACI DAN YEN MAI

0

KO ANYI AMFANI DA KAMFANIN A A RANO AN SACI DAN YEN MAI. .? Rahoton point blank. Fassara jaridar madafa.
Yadda kamfanin Sahara Energy da kamfanin AA Rano oil suka Sace $ 2.5billion na danyen mai a China, aka rarrabawa makusantan Buhari kudin.

Marigayi shugaban Ma’aikatan fadar Shugaban kasa Mallam Abba Kyari, ya yi amfani da wasu kamfanonin mai guda biyu na Najeriya, Sahara Energy da AA Rano Oil don sayar da ganga miliyan 48 ba bisa ka’ida ba da ya kai dala biliyan 2.5, sakonnin bayanai da aka samo daga jaridar Pointblanknews.com suka ruwaito.

Man, wanda aka sace daga Najeriya a shekarar 2015 an adana shi a gonaki da dama a Qingdao da wasu biranen China.

A baya dai jaridar Pointblanknews.com ta ruwaito cewa danyen mai da aka kiyasta ya kai dala miliyan 800. Ko da yake, wata majiya mai zaman kanta a yarjejeniyar ta tabbatar da cewa gangar danyen Bonny miliyan 48 da aka sayar wa Sinawa ya dara dalar Amurka biliyan 2.5.

Marigayi Shugaban ma’aikatan Buhari, Mallam Abba Kyari, Babban Manajan Daraktan Kamfanin Man Fetur na Najeriya, NNPC, marigayi Maikanti Baru, Ministan Shari’a Abubakar Malami, Saleh Mamman, da GMD na yanzu, NNPC, Mele Kyari sun kasance basu bin doka a yadda rahoton ya nuna.

See also  ME KAMFANIN GREEN HOUSE YAKE BOYEWA NE? (1)

An kuma bayar da rahoton cewa sunyi ruwa da tsaki wajan bayar da mukamin dakataccen Shugaban Hukumar Yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, Ibrahim Magu, da Air Commodore Mohammed Umar Rtd, da kuma tsohon Darakta Janar na Ma’aikatar Tsaro ta kasa Mallam Lawal Daura.

Wata Majiya mai tushe game da wani mai rahoto da ba’a bayyana shiba, ya shaidawa jaridar Pointblanknews.com cewa marigayi Abba Kyari bayan da ya tabbatar da kasancewar danyen mai da aka sata a China, ya umarci GMD na NNPC na yanzu, Mele Kyari, wanda a lokacin shi ne Babban Manajan Daraktan Rukunin, Crude. don karɓar danyen da aka adana a cikin manyan tankuna a China.
Mun Ciro daga fassarar jaridar Madafa dake a Facebook. Ba ragi ba kari

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here