Komawar Yan PDP Zuwa APC A Katsina Abin Da Ba Fada Ba!

0

Daga Danjuma Katsina

A makon da ya gabata ne ranar asabar aka yi wani gagarumin buki a Katsina na amsar wasu jiga jigai daga jam iyyar PDP Zuwa APC wanda cikin jiga jigan akwai tsahon kakakin majalisar dokoki na jahar katsina da yan majalisar su goma sha takwas da wasu tsaffin kwamishinoni da tsaffin masu ba tsohuwar gwamnati shawara da tsaffin ciyamomin kananan hukumonin PDP da wasu jigagai daga jam iyyun APGA DA PDM.

Taro ne wanda yayi taro hanyar zuwa filin wasa ya cika ya batse. Koda yake filin taron baiyi cikar da ake zato ba. Kamar yadda duk wanda yaje dandalin taron ya gani da idonsa. Da kuma wani hoton bidiyo wanda aka rika nuna ta sama kuma wanda yayi yawo a yanar gizo ya tabbatar.

Hakika taron ya zo a lokacin da bai dace da a yi shi ba. domin a satin ma aikatan lafiya suka gudanar da taron manema labarai suna neman a biyasu wasu hakkokinsu da ba a biya su ba. wanda kuma suke cewa ; aikinsu da sukeyi bai taba tsayawa ba dare ba rana kuma kudin da suke nema na hakkokin nasu bai taka kara ya karya ba.

A kuma watan ne ma’aikatu na jahar ke a cikin juyayi cewa an rage masu kudaden gudanarwa na tafiyar da ma aikatunsu. Wanda wasunsu sun rage ma aikatansu na wucin gadi ,wadanda suka yi shekaru suna gudanar da rayuwarsu daga wannan aikin da kuma kuma abin da suke samu daga alawus na aikin.

A kuma watan ne ma aikatan wucin gadi na kananan hukumomin jahar suka cika watanni takwas ba a biya su ba. wanda wasunsu suna shirin fara zanga zangar lumana amma wasu dattawa a jahar suka basu hakuri.

A satin ma aikata na tunanin halin da zasu shiga in wani kuduri da majalisar jahar ta zartar na mika al amarin fensho na ma aikata ga kamfanonin fensho. Masu zaman kansu. Wanda a satin majalisar zartaswa ta jahar sun zartas cewa gwamnatin jahar ta amince da rahoton wani kwamiti karkashin ofishin sakataren gwamnatin Katsina ya gabatar cewa. A mika al amarin fenshon ma aikatan jahar ga kamfanonin fensho masu zaman kansu , wanda aka tura lamarin ga majalisar dokokin jaha don ya zama doka.

Watan da kuma satin yana cike da lamurra abin tattaunawa a jahar sai kuma aka biyo shi da ana bukin amsar wasu da aka kira sun chanza sheka. Daga wata jam iyya zuwa wata. Buki ne wanda akayi a lokacin da bai dace da yinshi ba.

Binciken da nayi wajen tsaffin yan APC wadanda akayi gwagwarmayar tare dasu sam basa farin ciki da wannan dawowar da ma bukin . musamman wadansu kalamai da gwamnan Katsina ya rika maimaitawa akan wadanda suka dawon ya fadi cewa;
‘’ wadannan riga ko gida bata burgesu ba sunzo bane don neman kwangila kudi basu dame su ba’’ injin gwamnan a filin taron.

See also  'Yan Majalissar Dokoki A Najeriya Na Wani Yunkuri Na Tsawaita Amfani Da Jarabawar UTME Zuwa Shekara 3

Wadanda suka dade a APC suna ganin cewa an maido abokan gabarsu da suka yake su ana kuma son a fifita su. Don har ana masu gorin cewa su sun shigo da arzikinsu.
Wata shela da aka rika yi har a wajen taron ta hassala wadanda suka dade a cikin APC Inda aka rika cewa. Yanzu daya suke da kowa ba wanda ya fisu basu fi kowa a jam iyyar APC. Wannan ya kawo guna guni da surutai da shan alwashi wanda ke fitowa daga bakin yan APC Da suka dade.

Wani lamari da ya tabbata shine kusan duk wadanda suka dawo babu wanda baida matsala da tsaffin yan jam iyyar APC Na yankin da ya fito . wanda wannan yasa wasunsu su ka fara nadama tun kafin ranar da akayi bukin baki daya na amsar su.amma babu yadda zasuyi saboda sun zama cikin tsaka mai wuya.

Hatta masu rike da mukaman siyasa na APC Wadanda ke cikin gwamnatin . basa farin ciki sosai wanda wasunsu suna ganin tasirinsu zai rage da shigowar wadannan tubabbun na PDP.
Wani lamari da ya karawa taron bakin jinni da rashin armashi shine na kudaden da ke zargin an kashe. Wani babban kwamitin karkashin sakataren gwamnatin Katsina Alhaji Mustafa inuwa shine wanda ya tsara da aiwatar da taron.

Ba wanda za iya cewa ga abin da taron yaci .amma ganin hidimar da akayi an san cewa kudi masu yawan gaske sun sha kashi . hatta mutanen da suka halarta sun rika labartawa a taron dauko su haya akayi don su halarta. Shi ya sa mafi yawansu su kayi zamansu kusa da motocinsu ba tare da zuwa filin taron ba. wasu kuma suka shiga gari yawo.
Taron mai makon ya janwo wa wadanda suka koma farin jinni bakin jinni ya jawo masu. Mafi yawansu sun rika samun tawaye daga jama arsu. Cewa suna zargin sun amso kudi amma basu basu wani abin kirki ba. Wannan yasa mafi yawansu basu kwana gidajensu ba bayan taron.

Rashin zuwan shugaban kasa MUhammadu buhari ko turo wakili ko sakon fatan Alheri a taron , ya farantawa yan APC akida na jahar rai da kuma yan APC masu adawa da bukin da kuma amsar yan PDP .

Ko dawowar yan PDP zuwa APC Zai wata tasiri? Lokaci ne zai tabbatar da hakan.
Danjuma Katsina. Marubucine/Mawallafi
Wannan sharhin ya fito a jaridun.. Aminiya..wakilya…da Al mizan

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here