Mai shari’a M. Itsueli na babbar kotun jihar Edo yayanke wa Ogundele Oluwaseun Solomon hukuncin zaman gidan gayran hali na shekaru biyu bayan ya kama shi da laifin zamba ta yanar gizo
Solomon mai inkiya da ( Rick Rick) ya amsa laifin sa ranar Alhamis, 1 ga watan satumba, 2022 bayan hukumar EFCC shiyyar Benin ta gurfanar dashi akan tuhuma daya.
Mai shari’a Itsuele ya yanke wa Solomon hukuncin shekaru biyu ko ya biya tarar Naira dubu dari biyu.
Source: EFCC