KOWA YA KARE KANSHI DAGA HARIN YAN BINDIGA

0

KOWA YA KARE KANSHI DAGA HARIN YAN BINDIGA….inji gwamnan zamfara
Daga Hussaini Ibrahim, Gusau
@ katsina city news

A cigaban da bukikuwan cika shekaru biyu da Gwamnatin gwamnan Zamfara,Hon Bello Muhammad Matawalle Maradun ya ba al’ummar jihar dama kare kansu daga harin ‘yan ta’ada,”Yan Bindiga da masu garkuwa da mutane.

Gwamna Matawalle ya bayyana haka ne a wajan wa’azin mako mako da gwamnatin kegabatarwa a kowace Juma’a.

Kuma ya kara da cewa, gwamnatin tayi iyakokarinta na gani an kawo karshe wadannan “Yan ta’ada abun yaci tura,sai kara yawaita abun keyi.dan haka na bada umarnin karekai a duk lokacin da akaji cewa,mahara zasu kawo maku hari a kauyuka ku.

See also  HARE HARE A SABUWA DA FASKARI Muazu hassan

Gwamnan Matawalle ya kuma tabbatar da cewa,duk dan ta’ada da aka kama ko meba maharan rahotan siri ya tabbatar saidai uwarsa ya hafi wani.

Matawalle ya kara kalubalantar “yan adawa siyasa akan cewa,Ida suna qaunar al’ummar jihar Zamfara su foto su bayyana wa al’umma cewa,masu da hannu ko jindadi da hare haren da ake wa al’umma jihar Zamfara.inji gwamnan Matawalle
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
Www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here