DAGA DAJIN RUGU
*KOWA YA YI FANSHI KANSA DA NAIRA DUBU 50*
Daga Husaini Jakada
Kauyuka da yawa da Jihar Katsina ‘yan bindiga suna yadda suke so. A kan haka muka tsara kawo maku labarai na yadda suke sheke ayarsu a inda suke watayawa.
Mun tsara ba shafin suna Daga Dajin Rugu. Mun kuma tsara boye sunan gari da mutanen da abin ya shafa don kiyaye lafiyarsu, amma duk labarin da za mu kawo sai mun tabbatar da ingancinsa, mun yi magana da wadanda abin ya shafa da ganau kuma shaidu.
Labarin yau: KOWA YA FANSHI KANSA DA NAIRA DUBU 50.
Wani jigon ‘yan bindiga ne da ke zaune cikin wani kauye tare da mutanen gari, kowa ya san ko shi waye, kuma ana shakkarsa da bin sa a hankali.
Wata rana za a debo masa ruwa a kura, sai ta yi faci, don haka sai ya ce a amso tayar wani makwancinsa a sanya wa kurarsa a kai masa ruwa a gida.
Bayan an kai ruwan, makwabcin nasa ya yi ta jiran a dawo masa da taya shiru, sai ya dauki tayar dan bindigar aka yi facinta, ya kuma je gidansa don ya ba shi tayarsa ya karbi tasa.
Dan bindigar ba ya gida a lokacin, sai makwabcin nasa ya fada wa ‘yan gidan abin da ya kawo shi. Sai suka yi shawarar ya cire tayarsa ya mai da wa dan bindigar tasa. Haka kuwa aka yi.
Da dan bindigar nan ya dawo aka fada masa abin da ya faru, sai kawai ya yi wata kara! A fusace ya nufi gidan makwabcin nasa ya kalubalance shi. Yana mai cewa shi a wa zai je ya cire tayarsa ba da izninsa ba?
Gardama ta sarke har makwabcin ya bangaji kirjin dan bindigar. Sai kawai ya kira waya. Kwatsam sai ga ‘yan’uwansa wajen su 20, kowa da bindiga a rataye!
Aka taru ana kallon ikon Allah! Sai dan bindigar ya ce wa makwabcin nasa: “Fanshi kanka da Naira dubu 50 yanzu, ko ka bakunci lahira”.
Sai wasu suka taso za su ba da hakuri. Sai ya ce: “Ku ma dubu 50”. Wasu ma suka kara tasowa, ya ce: “Ku ma dubu 50”.
Aka yi carko-carko. Can sai aka ce aje a fada wa Limamin gari.
Liman ya sanyo rawani da abaya ya zo ya ce: “Haba wane! Ya za ka yi haka?” Liman ya shiga nasiha.
Can dan bindigar nan sai ya ja numfashi ya ce saboda Liman ya sanya baki, duk wadanda ya yi wa tarar dubu 50, ya yafe masu.
Shi kuma babban mai laifin an daga masa kafa, maimakon yanzu-yanzu, ya kawo dubu 50 din cikin mako daya in yana son ya ci gaba da rayuwa.
Yana fadin haka sai ya ce wa sauran ‘yan bindigar su tafi, shi ma ya juya ya koma gida.
Kafin mako gudan ya cika aka kawo masa dubu 50, ya kirga ya ga sun cika. Ya kawo Naira 500 ya ba makwabcin nasa ya ce ya sai wa yara alawa.
Wannan ita ce rayuwa a Dajin Rugu, wato inda ‘yan bindiga ke da tasiri a Jihar Katsina.
Katsina City News
@www.katsinacitynews.com.
Jaridar Taskar Labarai
@ww.jaridartaskarlabarai.com
The Links News
@www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245