KUNGIYAR DALIBAN AREWA SUN KARRAMA RARARA.

0

KUNGIYAR DALIBAN AREWA SUN KARRAMA RARARA.

A yau ne wata kungiyar daliban arewacin Nijeriya mai suna ‘Association of Northern Nigerian Students’ (ANNS) suka karrama fitaccen mawakin siyasar nan wato Dauda Kahutu Rarara.

ANNS kungiyar dalibai ce wadda ta kunshi jihohin Arewa goma 19 da kuma babban birnin tarayya Abuja. Daliban sun ba Rarara lambar girmamawar ne a harabar Otal din Tumfure da ke garin Gombe.

Da ya ke yi Kannywood Exclusive karin bayani game da karramawar, shugaban gudanarwa na kungiyar na shiyyar arewa maso gabas, Kwamred Sadik Sabo ya ce: “Ita daman kungiyar mu ta kan yi duba a cikin al’umma ta zakulo wani mutum, wanda ya kware wajen yi wa al’umma hidima a kasa baki daya.

Wannan kungiyar ta zakulo Rarara, kuma an zauna an ga cancantar sa, kafin a karrama shi. Shi ya kasance tsaka tsakiya tsakanin talakawa da gwamnatin kasar nan. Wanda ko a rediyo ba lallai ne ka san yanayin da kasa ta ke ci ba.

See also  wasikar da farfesa sani Abubakar lugga ya rubuta ma masauratar katsina,

Amma cikin baiwar da Allah ya ba shi, ya kan dauki korafe-korafe na talakawa sannan ya isar da sakon su ta sigar waka, kuma sakon sa yana isa a wurin ‘yan siyasa, wanda idan su ka ji matsalolin sai su duba, su ga ta inda za su fara gyara.

A gefe guda kuma shi wannna mawakin gwani ne da ya shahara wurin hidimar al’umma, a ko’ina za ka gan shi, ba za ka gan shi shi kadai ba sai da dandazon al’umma. Maganar gaskiya idan mutum ba mai alheri ba ne, ba lallai ba ne ka ga jama’a na dabaibaye shi ba. Wannan yana daga cikin dalilin da yasa wannan kungiya ta mu ta karrama shi domin kara masa kwarin gwiwa bisa ayyukan da ya ke yi na ci-gaban al’umma da kuma talakawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here