Kungiyar Marubuta ta jihar Kano ta yi sabbin Shugabanni

0

Kungiyar Marubuta ta jihar Kano ta yi sabbin Shugabanni

Ƙungiyar Marubuta ta ‘Kasa (ANA) Reshen Jihar Kano ta gabatar da zaɓen sabbin shuwagabanninta a yayin gudanar da taronta na shekara-shekara wanda aka yi a ɗakin taro na American Space da ke cikin babban ‘Dakin Karatu na Murtala Muhammad a unguwar Nassarawa GRA Kano ranar 29 ga watan Mayu, 2021.

An gudanar da za6en ne k’ark’ashin jagorancin Dr. Maryam Ali Ali. Sabbin shuwagabannin da aka za6a kuwa su ne:

Tijjani Muhammad Musa – Shugaba
Maimuna Idris Beli – Mataimakiyar Shugaba
Mazhun Idris – Magatakarda
Yasir Kallah – Mataimakin Magatakarda
Ma’aji – Ɗanladi Haruna
Sakataren Kud’i – Abdullahi Lawan Kangala
Jami’in Yad’a Labarai (Hausa) – Ibrahim Muhd Indabawa
Jami’in Yad’a Labarai (Turanci) – Aliyu Abdullahi Muhammad
Jami’ar Walwala – Umma Sulaiman ‘Yan’awaki
Mai Binciken Kud’i ta 1 – Bilkisu Yusuf Ali
Mai Binciken Kud’i ta 2 – Sadiya Garba Yakasai
Mashawarci kan Shari’a – Hassan Ibrahim Gama

See also  NEW ACCOMMODATION AND MEDICAL FACILITY FOR TROOPS AT MAIMALARI BARRACKS IN BORNO STATE!

Shugabanni Marasa Gafaka: Zahraddeen I. Kallah, Abba Shehu Musa, Dr. Murtala Uba da kuma Rufaida Umar Ibrahim

Dukkan waɗanda aka zaɓa za su yi aiki ne na tsawon wa’adin shekaru biyu.

Kwamitin Zaɓe: Dr. Maryam Ali Ali (Shugaba), Kabiru Yusuf Fagge (Sakatare), Jamilu Haruna Jamilu (Mamba)

Sanarwa, Ibrahim M. Indabawa
Magatakarda

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here