KUNGIYAR MATASA MABIYA DARIKUN SUFAYE SUNYI ALLAH WADAI DA MUZANTA SHIEK ALI PANTAMI DA AKAYI

0

KUNGIYAR MATASA MABIYA DARIKUN SUFAYE SUNYI ALLAH WADAI DA MUZANTA SHIEK ALI PANTAMI DA AKAYI

Wannan kungiya ta yi Allah wadai da mummunan cin zarafin da wata kungiyar adawa ta siyasa ta kaiwa babban malamin addinin musulunci kuma jagora wato sheikh isa Ali pantami,ministan sadarwa da fasaha na kasa a ranar talata 23/9/19 a filin tashin jirage na malam aminu kano da ke jihar kano a kan hanyarsa ta komawa abuja bayan ya gabar da ta’aziyyarsa ga Hon Sha’aban Ibrahim sharada shaaban kwamitin majalisar tarayya kan sha’anin tsaro bisa rashin mahaifinsa da ya yi a sharada cikin birnin kano.

Sannan kuma muna kira da babbar murya ga su jagororin wannan kungiya da su gaggauta ba da hakuri a kan abinda ya faru.

See also  EFCC Ta Kama Dattijo Da Ake Zargi Da Handame Dukiyar Magada Har Miliyan 12

Kuma mu na so mu yi amfani da wannan dama wajen mu yi kira ga duk alummar musulmi na kowanne bangareko aqida da su fito su yi tofin Allah tsine kuma su yi Allah wadai ga wannan danyan aiki da su ka aiwatar.
Signed by
_____________________
MUSLIHU YUSUF ALI
national Secretary

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here