Kungiyar Matasa Na Goyon Bayan Dakatar Da Mai Shari’a Na Kasa

0

Kungiyar Matasa Na Goyon Bayan Dakatar Da Mai Shari’a Na Kasa

GAMAYYAR kungiyoyin matasa na kasa sun hadu a Kaduna yayin wata gagarumar zanga zangar da suka kira domin su Nuna goyon bayansu ga matakin da wata kotu ta dauka na dakatar da babban Mai shari’a na kasa mista Onnonghen.

Ita dai wannan kotu ta dauki matakin bayar da umarnin shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya dakatar da shi ne biyo bayan sabawa dokar kasa da ya yi na kin bayyana wa kotun kula da da’ar ma’aikata da kuma samun sa da laifin mallakar asusun ajiya a kasashen waje wanda yin hakan ya Saba wa dokar kasa.

Su dai wadannan matasa sun yi tururuwa ne inda suka hallara a babban filin taro na tunawa da Murtala da ke cikin garin kaduna domin Nuna goyon bayansu ga matakin da aka dauka.

Su dai Matasan maza da mata karkashin kungiyoyin matasa irin su Matasan arewacin Nijeriya (NYN), gamayyar kungiyoyi matasa (UNYF), kungiyar Matasan Arewa (AYA) da kuma kungiyar Matasan Arewa masu Yaki da masu kokarin yin cin hanci da karbar rashawa (NYAA).

See also  An Maka Sarki A Gaban Kotu Kan Rabon Gado

Matasan dai sun dauki kwalaye masu dauke da rubuce rubuce kamar haka Muna son Shugaba Buhari ya ci gaba da jagoranci har bayan shekarar 2019, Ba ruwanmu da masu yin kasuwanci da batun shari’a don haka Sai Karshen kasuwanci da shari’a, Sai kuma wasu da suka rubuta Muna godiya ga BUHARI domin shi wani lamari ne daga Allah.

Ya fa dace mutane irin su Onnonghen su sani cewa dubu ba zai taba zama daidai da gaske ba kuma masu kokarin goyon bayan karya suna kokarin danganta lamarin da siyasa Ko batun zaben da ke zuwa lallai ya dace su canza tunani.
Lamarin dakatar da wannan babban Mai shari’a na kasa na kara dumama harkokin siyasar Nijeriya Baki Daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here