Kungiyar TBO Na Daga Matsalar Buhari

0

Kungiyar TBO Na Daga Matsalar Buhari

Daga Taskar Labarai

Wani littafin da ya fito kwanan nan mai suna da Turanci POLITICS AS DASHED HOPES IN NIGERIA. Wanda Dakta Auwalu Anwar ya rubuta ya bayyana wani babi na littafin yadda kungiyar nan ta kamfen din Buhari mai suna TBO ta zama matsala ga duk takarar da yayi tun daga 2003 har zuwa 2015.

Marubucin ya kawo daki-daki yadda TBO ta rika nuna tafi karfin uwar jam’iyya da kin biyayya ga kowane babba a jam’iyyar ko tafiyar ta Buhari.

Da kuma yadda Buhari ya sanya masu ido ba tare da taka masu burki ga ayyukansu ba.
Marubucin ya kawo yadda da dan TBO ya nemi wata bukata a wajen gwamnan APC bai samu ba, sai kawai yaje ya bata shi a wajen Buhari kuma sai su fara kamfen na bata masa suna kowanene shi.

Marubucin ya kawo yadda ‘yan TBO suka haddasa fada da gaba tsakanin gwamnan Kano Shekarau da Buhari.
Har ya kawo wani labarin, mai burgewa, a lokacin ance Buhari yayi amfani da Nuhu Ribadu shugaban EFCC suka rubuta wata takarda ga Obasanjo suna neman a basu iznin su ayyana cewa Shekarau bai cancanta yayi takara ba, karo na biyu.

Obasanjo sai ya gayyaci Shekarau fadar shugaban kasa ya kuma kira Ribadu, suna haduwa sai Obasanjo ya nunawa Shekarau abin da Ribadu ya rubuto, sannan a nan take yace ma Ribadu kaje ka canza wannan takardar.

See also  TARIHI DA DALILAN YIN BIKIN TAKUTAHA A KANO

Nan Ribadu duk kunya ta kama shi. A littafin an yi zargin cewa Buhari ne ya zuga Ribadu ya rubuta waccar takardar
Da suka fito Ribadu ya biyo Shekarau yana bashi hakuri, yana fada masa cewa dalilai ne, suka sanya ya rubuta waccar takardar ga shugaban kasa.

Marubucin ya kawo yadda Shekarau ya fada masa cewa Buhari ya kira shi har Kaduna yace, kar ya yarda da labarai da ake yadawa cewa wai shi ne yake zuga ana bata masa suna.

Yace kuma duk abinda Obasanjo zai fada masa kar ya yarda, don Obasanjo ya iya haddasa fitina da rura wutar gaba.

Littafin yace manyan ‘yan TBO guda biyu sun rika fada da shekarau ne, don anki biya masu wata bukata na farko Hajiya Naja’atu Bala Muhammad ta nemi bukatu har guda biyu ana kin yi mata sai ta ajiye mukaman da aka bata ta fara fada.

Na biyu kuma wani janar da marubucin bai ambaci sunansa ba, wanda daga cikin bukatar sa harda Shekarau ya rusa majalisar zartaswar sa a sake lale.

A littafin an bada labarin yadda Attahiru Bafarawa ya bada cin hanci ga shugabannin jam’iyyar APP don su zabi Buhari yayi takarar shugaban kasa a Inuwar jam’iyyar a 2003.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here