LAƘABIN WASU FITATTUN MAKAƊAN HAUSA A DUNIYAR WAƘA

0

1- HARUNA (UJI).
Sunansa na yanka Haruna, wato sunan wan mahaifinsa, Malam Haruna. Malam Haruna yana da mata mai suna IYA KURA, lokacin da Haruna Uji yana ƙarami, matan ƙanin mahaifinsa suna masa wasa suna ce masa mijin Iya Kura, mijin Iya Kura.
A wannan lokacin yara ƙanana da ba su da baki, sai suke ce masa, Ujin Iya Kura, maimakon mijin Iya Kura. Wannan shi ne asalin inda Haruna Uji ya samo Inkiyar Uji. Tun ana danganta sunan da mijin Iya Kura, har aka daina, ake cewa Ujin Iya Kura.

2- IBRAHIM (NARAMBAƊA).
An haifi Narambaɗa a garin Tubali kuma a nan ya yi karatu, ya yi rayuwarsa gaba ɗaya. Mahaifiyar Narambaɗa kuwa makiɗiya ce, don haka a iya cewa ya yi gadon kiɗa ne daga wurinta.
Ya samu sunan Narambaɗa ne dalilin wata karyarsa (macen Kare) da ake ce wa Rambaɗa, don haka sai aka yi masa laƙabi da Narambaɗa.

3- MUHAMMAD BAWA (ƊAN’ANACE).
An haifi Muhammad Bawa Ɗan’anace a garin ‘Yar tsakuwa ta ƙasar Gandi, wadda ke ƙaramar hukumar Raba a yanzu. Mahaifin Ɗan’anace ba mawaƙi ba ne, manomi ne. Ɗan’anace ya koyi ƙida ne a wurin ƙanin mahaifiyarsa, wato Anace, wanda ya taso a hannunsa. Shi kuwa Anace, wani shahararren makaɗin ‘yan dambe ne, kuma shi ne sarkin ƙidan ‘Yar tsakuwa a wannan lokaci. Saboda tashin da ya yi a hannunsa ne, yasa ya fara sana’ar kiɗan dambe, tun Anace na da ransa, wannan yasa ake masa laƙabi da Ɗan’anace.

See also  KARIMCIN KUNGIYAR YANKASUWA GA ALH DAHIRU MANGAL (GOC NA ALHERI).

4- MUSA (ƊANKWAIRO).
Musa ya samu wannan laƙabi na ‘Ɗankwairo’ tun lokacin mahaifinsa na raye. Mahaifinsa yana da wani yaro da ake ƙira Ɗankwairo saboda zaƙin muryarsa da kuma ƙwarewa wajen yin waƙe, sai Musa ya rinka kwaikwayon sa tare da kwaikwayon muryarsa. Ganin cewa Musa ya ƙware kamar shi Ɗankwairon na asali, sai ake kiransa da wannan laƙabi na Ɗankwairo.

5- ADAMU (ƊAN MARAYA).
An haifi Adamu Wayya wanda aka fi sani da Ɗan Maraya a 1946, inda hakan ke nuni da cewa ya rasu yana da shekara 69 ke nan, sai dai waɗansu na kusa da shi sun bayyana cewa ya kai shekara 80.
Mahaifin Ɗan Maraya mawaƙi ne, ɗan Sakkwato, bayan yaje Bukur ta Jihar Filato ya yi waƙa a fadar Sarkin Bukur, Sarkin ya buƙaci ya zama mawakinsa, a lokacin an je da Ɗan Maraya a goye, sai dai ba a jima ba mahafinsa ya rasu, sannan kuma mahaifiyarsa ta rasu tun bai yi wayo ba, hakan ya sanya ake ƙiransa da Ɗan Maraya.

Muhammad Bala Garba.
19 Satumba, 2020.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here