LABARIN GWAGWARMAYAR KAWAR DA SOJA DA KAWO FARAR HULA A NAJERIYA

0

LABARIN GWAGWARMAYAR KAWAR DA SOJA DA KAWO FARAR HULA A NAJERIYA

Daga Danjuma Katsina

Wani littafi da Kayode Fayemi ya rubuta da Turanci mai suna OUT OF THE SHADOWS in da ya bada labarin yadda yayi gwagwarmaya lokacin mulkin Abaca don tabbatar da maido da mulkin farar hula.

A littafin ya kawo sunan wasu da suka rika bada nasu gudummuwar daga arewa, ciki har da sunayenmu, kamar yadda ake kiranmu a zamanin wancan gumurzun mu uku daga arewa muka rika baiwa gidan rediyon Kudirat rahoto a labaran su na Hausa.

Labari ne, mai tsawo da darussa wanda na taba rubuta shi har aka buga a jaridar Almizan a wani rubutu na ta’aziyyar Malam Ibrahim Usman Wanda mukayi aikin tare.

Malam Ibrahim Usman sojoji suka kashe shi a zariya a 2015 dan jarida ne, da yayi aiki wuraren da suka hada da rediyon Kaduna, mujjalar Hotline da Rana da Redio kudirat da sauransu.

Marigayi MD Yusufu, ya hada ni da Tajuddin Abdurrahim mai kula da sashen Hausa na rediyon. Yace in taimaka masu ni na jawo Ibrahim Usman da Sani Gataka muka rika aikawa da me ke faruwa a arewa? Su kuma su watsa da Hausa da Turanci da Ibo da Yarbanci da Turancin da fijin.

Mun yi aiki cikin hatsari saboda lokacin kisa ne, ba zuwa kotu, aji kana aika ma rediyon rahoto. Wadanda suka yaki mulkin soja sun kasu kashi kashi, yan kudu, wadanda wasu sukayi gudun hijira a lokacin irinsu Bola Tinubu, Kayode Fayemi da Sawore mai gidan jaridar Sahara reporters da sauransu.

Mafi yawan su suna cin gajiyar dimokaradiyar da aka yi yakin a kawo. ( sun rike mukamai ko suna rike da mukaman)
Hatta su CIF ganiyu Adams .shugaban OPC da aka horas da su a kasar Ghana yadda ake tada bore da kayar baya ga mulkin soja duk suna cin gajiyar gwagwarmaya da aka yi.

See also  FG says N1bn solar street lights project in Adamawa fully executed

‘Yan arewa wadanda muka bada tamu a jaridance, sai dai a rika kawo sunayenmu a rubuce-rubuce mun sadaukar a lokacin muna matasa yan shekaru kadan.

Tajuddin yana shirin yazo ya yawata damu ga sauran yan gwagwarmaya sai yayi hatsarin mota ya mutu a kasar Kenya (koda yake anfi zargin kashe shi akayi) a 2006.

Marigayi MD Yusufu ya taba gabatar damu ga Bola Tinubu, Wale Soyinka da Frank Kokori da Kayode Fayemi da Obasanjo, amma gabatarwar iyakarta a wani taron cin abinci da akayi a Legas gidan Tinubu a 2009.

Kodayake lokacin, muna da namu dalilan na hada kai dasu a gwagwarmayar, abinda na kan tuna in ji dadi shi ne a rubuce yake a tarihin ganin soja ya bar mulki an baiwa farar hula, nima na taka tawa rawar. Wanda in ana rubutu ana kawo wa.

Littafin OUT OF THE SHADOWS shi ne littafi na hudu da ya kawo har da sunayenmu da abin da mukayi, nima ina rubuta nawa na Hausa da Turanci da na sanya wa suna GUDUN HIJIRA A BIRNIN KANO.( na Sanya masa sunan ne don daga Kano muka rika gudanar da ayyukanmu) Zan kuma sadaukar da littafin ga marigayi Alhaji MD Yusufu. (Allah ya jikinsa da Rahama ya kyauta ta bayansa)

Nayi magana da tsohon shugaban kasa Obasanjo ya amince zai mani gabatarwa in na rubuta bisa wasu sharruddan da ya gindaya.

Ga mai bukatar littafin na Kayode Fayemi na sayarwa akwai shi a Matasa Media Links, a kan farashin naira 2500 kacal.( naira dubu biyu da dari biyar).yana da shafuka 483
Zaka ji labarin yadda ake tada kayar baya a hana gwamnati zaman lafiya.in taso tayi zalunci.damu akayi zamanin soja
Da kuma jaridar Al mizan wadda a lokacin ita kadai ce jaridar Hausa dake fitowa duk jumma a.
Amma ana sayar da ita kamar yadda ake safarar hodar iblis.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here