Labarin Soyayyar Laila Da Majnun .Daga Salahudden Uthman Idris

0

Tarihi
Labarin Soyayyar Laila Da Majnun
.Daga Salahudden Uthman Idris

Waye Majnun lailah? Wani mutum ne da aka yi a daular Banu Umayyad a bisa zance mafi inganci.
Sunansa shine Qais Bn Mulawwah daga labilar Banu Amir, Qais Balarabe kauye ne, ya taso tare da ‘yar gidan kawunsa mai suna LAILA BNT MAHDI IBN SA’D amma an fi sanin Laila da sunan Laila Aamiriya, tare suka taso tun suna yara suna kiwon
dabobi har suka girma, suka fita daga sahun yara suka kai munzalin balaga.
A Yayin da alamun nuna balaga da cikar budurci suka gama bayyana a jikin Laila sai Qais ya rude soyayyarsa gare ta, hankalinsa ya dugunzuma ya tashi.
Domin a wannan lokacin ne Qais ya lura da
irin kyawun dirin da Allah Ya yi wa abokiyarsa Laila, a kullum soyayyar Laila sai kara tashin gwauron zabi take yi a cikin zuciyar Qais, a cikin wannan yanayi ne Qais ya shiga rera mata wakokin soyayya kala-kala babu dare babu rana hakan ce ta sa Mahdi mahaifin Laila ya nemi da Qais ya fito dan maganar aure, saboda nuna soyayya da kauna sai Qais ya bayar da rakuma hamsin gidansu Laila a matsayin kudin aure.
Ana haka sai ga wani mutum da ake
kira WIRD BN MUHAMMAD wani dan hamshaqin attajiri ne daga cikin ‘ya’yayen masarautar Banu Umaiyya, katsahan ya yi ido hudu da Laila a wata rana a cikin wani Lambu tana kiwon dabobinta.
Daga wannan rana soyayyar Laila ta hana
Wird ya yi bacci a wannan dare! Cikin ‘yan kwanaki kadan iyayen Wird suka sauka a gidan su Laila dan neman aurenta ga dansu Wird.
A wannan rana da iyayan Wird suka je ga mahaifin Laila Said a suka ajiye masa manyan rakuma guda dari (100) a matsayin kudin aure, watau ribi biyu akan abinda Qais ya bayar!
Daga nan lissafi ya kwace wa mahaifin Laila, domin kuwa ya yi irin mugun abin kunyar nan na nuna kwadayi da son abin duniya. Bayan haka ne mahaifin Laila ya kira ‘yarsa Laila cikin daki ya nai mata
hudunbar cewar ga mai kudi dan masu mulki shi zai aura wa ita!
Babbar Magana! Laila ta ki amincewa
da maganar mahaifinta a karon farko, amma sai ya yi mata barazanar cewar zai yanka ta idan har bata amince da auren Wird ba!
Kwatsam sai aka wayi gari Qais ya ji gari ya dauka da kace nace din an yi wa masoyiyarsa Laila aure, da Wird. Wanne irin hali Qais zai kasance a wannan ranar?
Tun daga wannan lokacin bacci yayi hijira
daga idonsa, farin ciki ya gagari zuciyarsa, damuwa bakin ciki gami
da bacin rai da takaici, zubar da hawaye babu dare babu rana, suka kasance tare da Qais a matsayin abokai na din-din-din! wake-waken soyayya sune zancensa, ba shi da abokin hira sai wakar da ya ke yi wa Laila ga kadan daga irin abinda ya ke cewa:
“Zuwa ga Allah nake kai kukan son Laila
kamar yadda maraya ya ke kai kukan maraicinsa zuwa ga Allah.
“Marayan da kafarsa ta karye ga shi kuma dangi sun guje shi Lallai rasa iyaye abu ne mai girman gaske.”
Haka Qais da aka yi wa lakabi da “Majnunu lailah” ya ke bin kwararo-kwararo da saman manyan duwatsu da bakin ruwa da cikin furanni yana rera wa Laila wadan nan baituka masu motsa zuciya bai gushe ba har sai da aka yi masa lakabi da “majnunu laila”
Duk da cewa itama Laila tana matukar son Qais(majnun) amma kuma hakan ba ya hanata ta wahalar da shi, a wasu lokutan ma har da yi masa wulakanci a lokacin da suke tare, baya ga yin amfani da mallake shi da ta yi wajen azabtar da shi, dama haka sha’anin mata ya ke shi ya sa Majnun awani baiti ya ce:
“Na ce da wani babban malami da na gamu da shi a Makka, don Allah ka ba ni labarin wacce take cutar da ni, a zamanin da take jiji da kai (saboda ina sonta) shin hakan da take ba laifi bane?” Sai Malamin ya fadawa Qais cewa: “Wallahi da sannu azaba za ta shafe ta kuma a duniya ma saita hadu da bala’i.” Daganan Qais ya ce, sai na kasa mallakar idona sai da hawaye ya zubo cikin sauri ya jika min aljihun rigata, sai na ce, Allah Ya yafe mata
laifinta duk da ya ke a duniya dan kadan ne samunta.
Qais ko Laila Majnun Bai gushe ba a cikin wannan hali har sai da ya samu tabin hankali. Domin ya kasance idan ya ga yara suna wasan kasa ya kan zauna tare dasu ya taro kasa ya rinyqa gina gida irin wanda
yara suke yi da kasa yana cewa cikin waka: “abokaina kuzo kuga gidana
ni da laila”….!
A yayinda al-amari ya tsananta sai mutane suka bai wa mahaifin Majnun wato Qais shawara da ya dauke shi ya kai shi Ka’aba (dakin Allah) ya umarce shi da ya roki Allah
ya cire masa son Laila! Amma saboda tsananin soyayya a yayin da suka je dakin Ka’aba sai mahaifinsa ya ce masa: kama tufafin Ka’aba ka roki Allah Ya cire maka son Laila sai Majnun ya kama ya ce: “Allah na tuba gare Ka daga dukkan laifi, amma ba zan tuba daga son da nake yi wa Laila ba.
A tajaice haka Majnun ya rayu cikin wannan yanayi na abin tausayi! Ita kuwa Laila tuni wanda ya aure ta
ya dauke daga kasar Saudiyya gabaki daya zuwa kasar Iraqi. Hakavitama ta rayu cikin wannan mummunan yanayi abinka da ‘ya
mace mai rauni sai da rashin ganin Qais ya haddasa mata ciwon zuciya
Daga nan ita ma ta kamu da ciwon zuciya saboda tsananin soyayyar Qais Majnun! Tana cikin wannan hali ne na rashin ganin
masoyinta Allah Ya karbi rayuwarta!
A lokacin da Majnun ya ji labarin
rasuwarta sai da ya je har kasar Iraqi ya nemi inda take, da inda aka binne ta, a makabartar da aka binne Laila a daidai gindin kabarinta ya tare. Ba shi da aiki sai kuka dacwakokin soyayya a gareta. Wata
rana da safe sai masu wucewa suka
hango shi (Qais-Majnun) ya kifa
cikinsa akan kabarinta, ko da aka zo aka duba sai aka tarar Allah Ya yi masa cikawa! Haka fa Allah ya ke jarabtar wasu a soyayya.
Daga shafin salahudden uthman idris….

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here