LITTAFIN RAHOTON MARASA RINJAYE: YUSUF BALA USMAN DA SEGUN OSOB

0

LITTAFIN RAHOTON MARASA RINJAYE: YUSUF BALA USMAN DA SEGUN OSOBA

Daga Danjuma Katsina

A 1976 shekaru 42 da suka gabata gwamnatin soja ta lokacin ta gayyato wasu masana 49 daga duk fadin kasar nan don su rubuta ma Najeriya ingantaccen tsarin mulki.

Daga cikinsu akwai malam Yusufu Bala Usman da Olusegun Osoba bayan zama na tsawon lokaci sai aka fitar da takaiman kundi guda daya na tsarin mulkin kasa.

Bayan kammala aikin, sai biyu daga cikin ‘yan wannan kwamiti suka lura akwai kura-kurai a cikin kundin da za a gabatar, suka kuma an karar da sauran ‘yan kwamitin wannan nukusan. Amma sauran membobin suka ki saurarensu.

Don haka, wadannan membobin guda biyu, sai suka fitar da rahoton su da suka sanya wa suna RAHOTON MARASA RINJAYE Akan kundin tsarin mulkin Tarayyar Nijeriya.

A wancan lokacin rahoton na wadannan membobin guda biyu da suka yi wa ‘yan uwansu 47 tawaye, ya zama abin tattaunawa a kasar nan.

Hatta a karatun aikin jarida muhawarar rahoton marasa rinjaye na 1976 na daga cikin abin da yakan zama lamarin misali da nazari da daukar darasi a cikinsa.

Gwamnatin tarayya a lokacin, tayi watsi da rahoton na marasa rinjaye, kuma aka ki amsarshi amma masu rahoton Yusufu Bala Usman da Olusegun Osoba masana da ‘yan jarida sun ci gaba da nazari da kuma tattauna rahoton.

See also  Nana Asmaʼu Shehu Usman dan Fodiyo

Tsarin mulkin yayi ta samun canji, kuma wani lokaci ana la’akari da wani sashen na rahoton marasa rinjaye ana sako shi.

Bala Usman ya rasu (Allah ya jikansa) abokin tarayyarsa a rahoton Olusegun Osoba, yana da ransa. Saboda muhimmacin rahoton a yanayin da ake ciki, ya sanya cibiyar CEDDERT dake Zaria ta sake buga shi, kuma Olusegun Osoba ya sake masa gabatarwa.

Kungiyoyi NLC da ASUU za sa hannu wajen gabatar da shi a ranar talata 23/April/2019 a jami’ar Legas da karfe 12 na rana.

Na samu kwafi har na karance shi kaf, shawarwari ne, da aka ki dauka wanda inda an dauke su da wasu matsalolin tsarin mulkin najeriya da ba a same su ba.

Wani darasi da rahoton ke da shi shi ne ka fadi gaskiyarka kuma ka tsaya a kanta komai jimawa tarihi zai baka shaida.

Zan halarci gabatarwar Insha Allahu, kuma zanyi tsarabar littafin Rahoton ga masu bukata a wannan gida.@ katsina city news $taskar labarai

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here