MA’AIKATA A JIHAR KADUNA ZA SU KOMA AIKI
Daga Ibrahim Hamisu, Kano
Labarai da ke fitowa daga jihar Kaduna na cewa Gwamnatin jihar ta bada umurnin Ma’aikatan jihar su koma aiki ranar litinin 20 ga watan Yulin da muke ciki tare da kiyaye dokokin cutar Covid-19.
Gwamnan jahar Malam Nasiru Elrufa’i ya sanar a shafinsa na Twitter.
Ta cikin sanarwar ya ce Ma’aikatan da ke mataki na 14 zasu rika zuwa aiki a ranakun litinin da Labara da kuma Juma’a.
Yayin da su kuma Ma’aikatan dake mataki na 7 zuwa 13 za su rika zuwa aiki ranakun talata da Alhamis daga karfe 9na safe zuwa 3 na yamma.