MACE MACEN KANO: ZAA MAKA GWAMNATI KOTU
Daga Ibrahim Hamisu
Tun bayan fara nan ta kulle da gwamnatin Kano da ta tarayya ta sanya a Kano ake samun mace-macen mutane a Kano wanda har yanzu aka kasa samun takamaimai musabbabi.
Wani lauya mai zaman kansa a Kano Barista Umar Alto ya sha alwashin gurfanar da gwamnatin Kano da gwamnatin tarayya a kotu a gaban kuliya mudin bata gano musababin mutuwar ba.
Barista ya ce ” Jamaa fa suna mutuwa ba adadi don haka ni ina bawa gwamnatin jiha da gwamnatin tarayya waadi na mako daya da lallai lalai ta yi bincike ta gano musabbabin wannan mace macen su kuma kawo hanyar da zaa bi a magance ta”
Ya kara da cewa ” kin yin hakan zai zama bani da zabi da ya wuce in maka su a gaban koto.
Waadin dai ya fara ne daga ranar Talata 28- ga watan Afililu na wannan watan da muke ciki.