Maimakon haska bidiyon karbar dalan Ganduje, da aikin da ka yiwa mutane ka haska – Ize-Iyamu ya caccaki Obaseki
Daga Ibrahim Hamisu
Dan takaran gwamnan jihar Edo karkashin jam’iyyar All Progressives Congress APC, Fasto Osaze Ize-Iyamu ya caccaki gwamnan jihar, kuma abokin hamayyarsa Godwin Obaseki.
Ya ce gwamnan ya nuna rashin hankali bisa haska bidiyon karbar Dalan Ganduje kan allon talla a Ring Road, cikin babbar birnin jihar, Benin.
A jawabin da Diraktan labaran yakin neman zabensa, John Mayaki, ya saki, ya ce abin kunya ne kuma munafurci ne abinda Obaseki yayi.
Indai baa manta ba, a yan kwanaki sinimomi a birnin binin sun haska bidiyon Gwamna Ganduje inda ya ke karbar Daloli, wanda shi ne shugaban kwamitin yakin neman zaben jihar.