Majalisar dokoki na jihar zamfara ta dage zamanta na yau Alhamis
Shu’aibu Ibrahim Gusau
Majalisar dokoki na jihar zamfara karkashin jagorancin Hon Nasiru Magarya ta bada sanarwan dage zamanta na yau sakamakon samun munmunar hadarin Mota a jihar
Hakan ya fitone cikin wata takar da me dauke da sa hannun daratta Janar na yada labarai na majalisar,Mustapha Jafaru kaura, ya Kara da cewa jadawalin tattaunawar na yau alhamis 27/08/2020 an dage shi zuwa Litinin mai zuwa.
Kaura ya Kara da cewa hakan ya faru ne sakamakon hatsarin mota mai hatsarin gaske Wanda ya faru jiya a hanyar Gusau zuwa Yankara ,wanda ya shafi mafi yawancin magoya bayan babbar jam’iyyarsu ta PDP a jihar.
wadanda yace sun zo tarbar mai daraja gwamnan jihar Hon Dr. Bello Muhammad MON Matawallen Maradun a lokacin da ya dawo jihar daga wani aiki na musamman a Abuja.
Yayin da yake gabatar da addu’o’i na neman gafara, Hon Nasiru Magarya ya ce yana ganin ya dace na dakatar da zaman na yau har zuwa mako mai zuwa ranar litinin Insha-Allahu.