MATASA DA SANA’ARSU: KABIR SA’IDU BAHAUSHE~~ Yadda da kai Matakin Nasara.
Tare da Abdurrahman Aliyu
#JaridarTaskarLabarai
A duk ranar Lahadi Jaridar Taskar Labarai zata rika kawo maku bitar wasu shahararrun matasa na kasar nan da sana’o’insu da kuma irin kalubale tare da nasarar da suka fuskanta a rayuwa. Domin su zama a bin koyinga matasan mu wajen dogaro da kansu.
Kabir Sa’idu Bahashe shi ne gwaninmu na farko a wannan shiri da zai dauki tsawon shekara guda ana gudanar da shi in Allah ya yarda.
Kabir Sa’idu Bahashe matashi ne mai jini a jiki wanda sunansa ya tumbatsa a sassa da dama na kasara nan, musamman ta fuskar shahararrar sana’arsa ta Sankiran zamani (MC) ko kuma shirin gidan rediyo da ya ke gabatarwa a gidan rediyon Vision FM da ke Katsina.
In kuma kai ma’abocin karanta jaridar Hausa ne a nan ma zaka san sunan Bahaushe ta fuskoki da dama, musamman makaranta jaridar Aminiya da Leadership Hausa a Yau.
Kafin Kabir Sa’idu Bahaushe ya kai inda ya kai a yau ya sha gwagwarmaya sosai a rayuwarsa wadda ya nuna jajircewa da hakuri, ya fara aiki a matsayin kyauta ko kuma wucin gadi a gidan rediyon Vision, irin hakurin da ya nuna da jajircewa da kuma yadda da kai shi kai shi ga cimma nasarar shi.
NASARORI
A bangaren sana’arsa ta Sankiran zamani (MC) ya fara shuhura ne a tsakanin shekarar 2014-2015 inda ya fara halartar bukukuwa da tarukan na musamman domin gudanar da wannan sana’a tasa.
A bangaren wannan sana’ar tasa ya halarci taruka da bukukuwa masu yawa, daga cikin su har da taron Mawaka da aka gudanar a 2017 wanda ya yi magana gaban tarin jama’a mabambanta da suka hada da manyan ‘yan kasuwa da jami’an gwamnati.
A bangaren tarukan siyasa Bahaushe ya halarci tarukan siyasa kuma ya yi magana gaban duk wani fitaccen dan siyasa a jihar Katsina tun daga gwaman har zuwa kasa.
Kabir Sa’idu Bahaushe shi ne shugaban kamfanin Kakaki Unique Award kamfanin da ya shahara wajen zakulo fitattun mutane da suka taka muhimmiyar rawa a rayuwa domin karamasu da kuma nuna muhimmancinsu ga jama’a.
Daga cikin hobbasa da Nasarar da Kabir Sa’idu Bahaushe ya samu a matsayin shugaban kamfanin Kakaki suna hada da shiraya tarukan Nishadi da ba a taba samun wani matashi da ya jagoranci shirya su ba a jihar Katsina, misali taron karammawa na AMMA da taron tunawa da Mamman Shata bayan shekara 20 da rasuwarsa.
Kabir Sa’idu Bahaushe matashi ne da ya kamata a ce matasa sun yi koyi da rayuwarsa domin dogaro da kai. Musamman yadda ya rike sana’arsa kuma ya bata muhimmanci, haka ya kamata kowane matashi ya riki sana’arsa ya kuma nuna muhimmancinta a ko’ina ya samu kansa.
Wani abun burgewa Kabir Sa’idu Bahaushe ya samu ilimi na kowane fanni, a bangaren addini zaka tabbatar da haka in kana sauraren shire-shirensa da yake gabatarwa a gidan rediyo. A bangaren boko Kabir Sa’idu Bahaushe ya na da digiri na Farko a fannin koyar da harshen Hausa. Yanzu haka kuma yana shire-shiren tafiya karin karatu.
Sana’arsa ta sankirarn zamani ta yi masa kome a rayuwa kama daga iyali motar hawa rufin asiri da sauran kayan bukata na rayuwa.
Fatan wannan rubutun zai zama makaranta ka wasu matasa domin koyi da rayuwar matashi Kabir Sa’idu Bahaushe wajen dogaro da kansu da kuma kirkirar wasu abubuwa da muke da su a da domin zamanantar da su.