Suleman Umar
@ katsina city news
Wasu mahaajjatan katsina da suka dawo daga kasa mai tsarki daga kananan hukumomin Dutsinma, kankia da Charanci sun.
ko ko da kuma tambayar me ya hana Dan takarar gwamna da jam iyyar APC ta tsayar kai masu ziyara a kasa mai tsarki?
Hajia Halima Abdullahi daga karamar hukumar Dutsinma tace mun samu labarin Dikko Umar Radda yana kasa mai tsarki domin aikin Hajji, Mun yi tsammanin zai kawo mana ziyara amma muka ji shiru.ko me ya sa?
Alhaji Amadu sani daga karamar hukumar charanci yace,kusan duk jihohin kasar nan yan takarkarin su da suka je aikin hajji sun kai ma mahajjatan jahar su ziyara.amma bada katsina. Gaban mu aka yi rika ziyarar,ana farantawa mahajjatan Rai.
Sabi u Usman daga kankia ya ce.Mun so ya karrama mu ya ziyarce mu, yaga lafiyarmu.ba sai ya bamu komai ba.amma bamu ganshi ba.ko sakon ayi aikin hajji lafiya, Babu.
Mahajjatan katsina abin yayi masu zafi, suna ganin yadda yan takarkari ke ziyartar mahajjatan su banda na jahar katsina.
Mahajjatan sunyi Kira da Dan takarar APC ya basu hakuri ko ya bayyana dalilan shi na kin kai masu ziyara. Alhali kuma yana neman kuri “unsu a zaben 2023.
Katsina city news
Www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
Www.taskarlabarai.com
The links news
Www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245