Muhammadu Sanusi II da Talakawa
Daga Dr Aliyu U. Tilde.
A kullum aka ga wani abu na ci-baya da takaici ya faru ga Arewa ko an zalunci wani dan’arewa, mutane sukan fito su yi ta ɓaɓatu cewa manyan Arewa sun yi shiru, sun kulle kansu cikin gidajensu da ƴaƴansu, ba mai magana don a ceci al’umma. Wannan kuka ya zama ruwan dare tsakaninmu.
To sai ga shi an sami wani sarki, babban sarki, mai hazaƙa, karatu da kishin jama’a, Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, tunda aka naɗa shi yake fitowa firi-falo yana bayanai da gargadi da ba da shawarwari kan abubuwan da suka shafi talakawansa. Zan ba da misalai biyu.
Na farko shi ne yadda ya soki cin bashin Naira tirliyan barkate daga ƙasar China don shimfiɗa layin dogo da zai riƙa zirga-zirga tsakanin wasu unguwannin garin Kano. Kowa ya san gaskiya ya faɗa kuma ya yi ne don talakawa. Inda don kansa ne da sai ya shiga cikin shirin shi ma a yaga masa nasa kason. Ya yi ne don talakawansa. Maganarsa a lokacin ita ta sa aka fasa batun bashin. Wannan ba ƙaramar gudunmawa ba ce ga al’umma.
Na biyu shi ne, duk da ya rage magana a kan abida ya shafi gwamnati afili, sai zaɓe ya zo. Gwamnatocinmu na Arewa sun saba tirsasa wa Sarakuna su sa hakimai da dagatai su marawa Gwamnati mai ci baya. Sarkin Kano ya ƙi yarda da ya sa baki a tirsasa wa talakawansa zaɓen gwamna mai ci yanzu – Mai girma Abdullahi Ganduje – a zaɓen da ya wuce. Ya ce a bar talakawa su zaɓi abin da suke so. Faƙat. Shi ne laifinsa a gun Gwamna da wajen shugabannin jam’iyyar APC wanda shi ya sa suka ƙyale yanzu Gwamnan ya ci masa mutunci.
Irin waɗannan abubuwa ba su yi wa Gwamnan Kano din dadi ba. Don haka, ya fito da dukkan ƙarfin gwamnatinsa sai ya ga bayan Mai-Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II. Ma’ana, don me zai riƙa shisshigi ya na yi wa gwamnati ƙafar ungulu game da manufofinta a kan talakawansa? Alhali kuma waɗannan manufofin munana ne.
Wallahi yau da a ce Ganduje ya yi nufin alheri ne ga talakawa, sanina da Sarkin Kano tun tsawon shekaru 40 da suka wuce, zai zame kan gaba wajen taimaka masa. Amma manufofin mugaye ne. Ta yaya zai goyi bayan gwamanti a kan kafirar aniya? Ganduje, wallahi, bai yi wa Sarki adalci ba. Ya sani.
To yanzu Gwamnan ya sake tado da wata kwantatta wacce duk mun shaida ya ce ta wuce a baya, wai yana binciken Sarkin a kan zargin almubazzaranci da kuɗin talakawa. Ra’ayi na a kan wannan magana lokacin da ta fito da farko shekaru biyu da suka wuce shi ne Sarki ya bari a gama binciken don kar a nan gaba a sake amfani da shi a tozarta shi. Da yawa suka ga kamar na ci mutuncin Sarki ne. Ilai kuwa, inji Sakkwatawa. Ga ranar ta zo!
Ra’ayina a yanzu shi ne tunda Gwamna a baya ya ce maganar ta wuce, to ba dattaku ba ne sam ya sake tado ta. Wannan hali ne na ƙaramta da rashin daraja da rashin mutunci. Ya nuna cewa bita-da-ƙulli yake yi wa Mai-Martaba kuma bai kamata a goya masa baya ba a wannan kafirar aniya tasa. In mai mulki zai yi amfani da ƙarfin doka ya ci zarafin wani, kowane ne, to dole ne a tashi a nuna masa ba daidai ba ne.
Abin mamaki shi ne yadda, in ka debe ɗaiɗaikun mutane, talakawan da Sarkin yake kare haƙƙinsu suka yi ƙuru suna kallon abinda ke faruwa ba tare da sun fito ta kafafe dabam dabam suna sukan wannan al-kafura, da balahira da mummunar aniya ta Gwamna Ganduje a kan Sarkin Kano ba. Suna gani aka ɗaiɗaita masarautar Kano amma ba abinda suka yi. A cikinsu ma har da masu murnar an yi haka.
Wannan ɗabi’a ta talakan Arewa ita ce ta sa tuntuni manya suke shiru in sun ga wata tsatstsama na faruwa tsakaninsa da talakwa ƴan’uwansa masu mulki. In manya sun sa baki sai ‘ya’yan talakawa da ke mulki su taka su yadda suka ga dama, su sa karnuka cikin mabiyansu su ci mutuncinsu da zage-zage – wai don me za su hana su rawar gaban hantsi, su ƙyale su su saci dukiyar jama’a, su yi kama-karya san ransu?
Tabbas, mu ƴaƴan talakawa, a shekaru 50 da suka wuce tunda aka ƙwace mulki daga hanun sarakuna aka ba mu, mun nuna, akasarinmu, ba mu da kishin kanmu, ba mu da amana, ba abinda muka sa a gaba sai sata. Ba mu da daraja, ba mu santa ba kuma ba mu yarda akwai mai ita ba. Wannan shi ya kai mu ga halin ni-ƴasu da Arewa ke ciki. Da mun riƙe amana, da yau Arewa ce abin koyi a Afirka gaba ɗaya.
Da ma a ce mun ɗauki hanyar gaskiya
Da ba talakka ko guda yau duniya.
Sai munka ɗau hali na ɓeraye ku ji
Buri a gun kowa ya kas Nijeriya.
Haƙƙi na milyoyin jama’a zai haɗa
Sannan ya sace don yana tsoron tsiya.
Kullum ya zauna yai tunanin can gida
Danga da yunwa sai ya tsoro zuciya.
Sata yake, ƙari yake, ba dakace
Buri wadata babu dawowar tsiya.
Yanzu haka Gwamna ya ba Sarkin Kano awa 48 ya amsa taƙardar tuhuma da ya aika masa, mataki da ya yi kama da wanda Rimi ya yi wa marigayi, Sarkin Kano, Ado Bayero a 1981.
Shiru kake ji. Ƙungiyoyin Arewa irinsu ACF da wanda talakawan Arewa suka ɗauka a matsayin macecinsu, Mai-Girma Shugaban Kasa, da gwamnonin Arewa waɗanda da su suka kawo sulhu tsakanin Sarkin da Gwamnan a baya, ba wanda ya ce uffan, ko ya kira Ganduje ya ja masa kunne ko ya ba shi shawara
Mu da ke muke ƙauyawa, ba ƴan Kano ba, za mu ga abinda talakan Kano, da wayayyun Kano, da ƴan’bokon Kano, za su yi a kan wannan lamarin. Za su kawo wa Sarkinsu da ke ƙoƙarin kare haƙƙinsu ɗauki ne ko za su noƙe, su yi zugum, su bari wasu marasa daraja su ci mutuncinsa, ƙila ma har da tafa musu? Allahu aalamu!
Wannan ya tuna mun da wani faɗa da aka yi muna yara ƙauyenmu. Kai ‘Rajish’ ka zo ka iske anan faɗa da Ado, wani ɗan yarsa, a fagen makaranta, an yi da’ira ana kallo, ana ta saɓa Ado ana tiƙawa da ƙasa. Sai kai ‘Rajish’ka keta mutane ka faɗa cikin fage, ka ce da kai za a yi, ka kai wa Ado dauƙi. Ganin haka Ado wanda da ma yake neman tsira sai ya koma cikin masu kallo. Da aka shiga tiƙa Rajish da ƙasa, sai Ado ya shiga cikin masu tafi, yana dariya. Chan da ‘Rajish’ ya ji wuya, sai ya keta mutane ya ari ta kare. Mutane suka bi shi da ele, ciki har da Ado.
Allah sa kar talakawan Kano su yi wa Sarkin Kano abinda ‘Ado’ ya yi wa dan’wansa ‘Rajish’. Ƙila ƴan birni su fi ƴan-ƙauye zumunci.
Dr. Aliyu U. Tilde
7 June 2019