MUN GA BALA’I: INJI ‘YAN GUDU HIJIRA A YANKIN FUNTUA.

0
  • MUN GA BALA’I: INJI ‘YAN GUDU HIJIRA A YANKIN FUNTUA.
    ~~~Wadanda ke taimaka mana..
    ~~~ Sanata yankin ya manta dasu
    ~~~Bamu da masaniyar taimakon sanata: mataimakin shugaban APC

Daga Taskar Labarai

Wata mata da ta tsira da ranta da kyar ta fada wa wakilin Rediyon DW cewa da ‘yan ta’adda suka biyo ta suna gudu da ‘yan uwanta ta haihu, ta duka cikin jinin haihuwa tana nade jaririn a zanenta ta dauka ta ci gaba da gudu. Matar wadda yanzu haka da take gudun hijira a wata makarantar firamare dake garin Faskari.

Wani bidiyo da wakilin na rediyon DW ya dauka wanda aka Dora shi a bisa shafin na rediyon Jamani ya gwada yadda yara kanana ke rayuwa a wannan sansanin ‘yan gudun hijira cikin halin kuka da ban tausayi.

A lokacin da wakilin na DW yaje wannan sansani ya iske mace mai ciki sama da talatin ta haihu a wannan makaranta ta firamare.

Mazauna wajen sun bayyana yadda masu rike da mukaman siyasa na yankin ke taimaka masu, misali Alhaji Bashir Ruwan Godiya mai ba gwamnan Katsina shawara akan harkar ilmi mai zurfi da kwamishinnan muhalli Da Dan majalisar jiha mai wakiltar su dama uwa uba gwamnan na Katsina. Duk suna tallafawa halin da suke ciki.

Wanda kawai suke takaicin da Allah wadarai da zaben sa shi ne mai mukamin sanata na yankin su ta shiyyar Funtua, wanda binciken Taskar Labarai ya tabbatar da cewa babu wani tallafi ba Jaje ba gudummuwa. Koda sako a yanar gizo yana masu addu’a basu taba gani ba.

Wata mata dake gudun hijira a Funtua da aka koro da ga karamar hukumar Sabuwa ta fadawa gidan rediyon BBC cewa tana gudun tserar ranta aka kashe mata ‘ya’ya guda uku.

Binciken Taskar Labarai ya tabbatar da cewa sama da ‘yan gudun hijira dubu biyu na a yankin na sabuwa. Kuma suna samun tausayawa na ‘yan siyasa da masu rike da mukaman yankin amma banda sanata mai wakiltar yankin basu gan shi ba, babu sakonsa ko na tausayawa ko jaje ko tallafi.

See also  ANYI GARKUWA DA MIJI DA MATA A TASHAR KADANYA, BATSARI

A wata makarantar firamare dake garin Dandume inda sama da ‘yan gudun hijira dubu biyu ke zaune. Wata mata ta fadawa jaridar The links news cewa rike mijin ta aka yi wani yaro cikin ‘yanta’adda yayi fuskanci da ita, tace gabanta wani ya kware gaban wata yarinya ya debi gashin gaban ta wai zai hada wani asiri, tace wasu kuma sun rika hada jini da maniyi na mace da gashin kanta wai zasuyi wani tsafi dashi.

Taskar Labarai ta tabbatar cewa ‘yan siyasa, daga kowace jam’iyya attajirai da masu rike da mukaman gwamnati suna taimaka masu daidai gwargwado, wanda kawai ba zuwa ba sako babu aike shi ne sanatan yankin su.

Binciken Taskar Labarai ya tabbatar duk halin da ‘yan gudun hijirar dake yankin Funtua suke ciki na bala’i da masifa suna addu’a ga duk masu taimakon su, amma suna koke da sanatan su.

Taskar Labarai ta tambayi Alhaji Bala Abu Musawa mataimakin shugaban jam’iyyar APC a shiyyar Funtua ko yana da masaniyar wani taimakon da sanatan yankin Alhaji Bello Mandiya ya baiwa ‘yan gudun hijirar dake yankin na Funtua? Alhaji Bala Abu Musawa yace a iyakar saninsa da kuma ofis na shi baya da wata masaniya. Ba a aike shi ba, bai san wanda aka aika ba.

Bala Abu yayi kira ga sanatan da ya dawo ya san halin da mutanen shi ke ciki, ya kuma tausaya masu da taimaka masu kamar yadda wanda ya gada sanata Abu Ibrahim ke yi lokacin da yake rike da wannan matsayin.

Taskar labarai ta buga waya da aika sako a wayar sanatan don jin ta bakinshi, duk babu amsa mun yi kokarin jin ko yana da masu tafiyar da harkokin jin ra’ayin jama’a a yankin na f6untua? Bamu samu ko daya ba.
________________________________________________
Taskar Labarai na bisa yanar gizo na www.taskarlabarai.com da sauran shafukan sada zumunta tana da ‘yar uwar ta Turanci mai suna The links news dake www.thelinksnews.com. duk sako a aiko ga 07043777779.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here