Mun Kware Wajen Shirya Magudin Zabe, Cewar Sanata Mantu

1

Daga Abdulrahman Aliyu

Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ibrahim Mantu, ya bayyana cewa wannan lokacin na yafiya ne da manta baya tare da tsaya tsayin daka domin maido da martabar Nijeriya.
Mantu ya ce yana da hannu cikin magudin zabukan da aka yi a baya.

Dan siyasar ya ce “ba dole ne sai na je rumfar zabe na sauya alkaluman zaben ba, amma mun bai wa jami’an hukumar zabe da jami’an tsaro kudi yadda idan sun ga wata dama da za su sauya sakamakon zabe domin ya taimaki jam’iyyarmu, sai su yi hakan.”

Sanata Mantu, wanda ya bayyana hakan a hirarsa da gidan talabijin na Channels TV, ya ce ya tuba daga aikata magudin zabe shi ya sa yanzu ya bayyana abubuwan da suka wakana a baya.

See also  takardun rahoton da shugaban Yan sanda na kasa ya bayar...ga mukaddashin shugaban kasa

Tsohon dan majalisar dattawan fitaccen dan jam’iyyar PDP wanda a lokuta da dama aka zarge shi da hannu wajen cuwa-cuwar siyasa, ciki har da zargin yunkurin sauya kundin tsarin mulkin Najeriya ta yadda zai bai wa tsohon shugaban kasar, Cif Olusegun Obasanjo damar yin ta-zarce a karo na uku.
Sai dai shi da Cif Obasanjo sun sha musanta zargin.

Haka kuma an zarge shi da amsar Kudi wajen iyalan Marigayi tsoho shugaban kasar Nijeriya Alhaji Umaru Musa Yar’adua wajen shirya taruka da hira da ‘Yan jarida domin tabbatuwar mulkinsa duk da bai da lafiya a lokacin.

Daga karshe ya tabbatar da cewa ba za a samu ingantattar gwamnati ba har sai mutane sun tsarkake zuciyiyinsu.

 

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here