MUNA GANIN BALA I..

0

MUNA GANIN BALA I..
……inji yan gudun hijirar Kankara
A Tsakanin alhamis 22/4/2021 zuwa yau litinin 26/4/2021.sama da garuruwa ashirin yan ta adda suka tayar a karamar hukumar kankara ta jahar katsina.
Wasu yan gudun hijirar suna a garuruwan Mabai da kuma dansabau. Kamar yadda ganau suka tabbatar ma da wakilanmu.
Garin Dan marke tsohuwa.da barwa da mattallawa.fako.gidan mai a gwagi.dauki da mai sabo duk sun gudo suna garin Dansabau.
Wasu kauyuka takwas dake kusa da garin mabai. Duk gudu sun komo mabai.
Yanzu haka wadannan garuruwan guda biyu na mabai da Dansabau cike suke da yan gudun hijirar da suka baro kauyukansu.
Wasu garuruwan da suka ki,tashi yan ta addar suna ta matsa masu.da hare hare. Ko a jiya lahadi 26/4/2021.sun je garin unguwar kudu inda suka tafi da mutane biyar.
Wasu mata da sukayi hira da mujallar cilqq TV. A garin mabai sun bayana yadda ake masu fyade.da cin zarafi in an kawo masu hari.
Cliqq TV ta dauko hoton wani karamin yaro dan kasa da shekaru biyu yana lasar kasa yana ci kamar abinci..saboda halin bala in da yake a ciki.
Yan ta adda sun zafafa hare haren su a kwanakin nan a yankunan, kanan nan hukumomin .kankara.faskari.da kuma Dandume..
A garin Dansabau rundunar soja dake da mazauni a garin sun shirya tsaf da shirin ko ta kwana.suna baiwa yan gudun hijirar kariya.
Ganau sunce sojojin dare da Rana suna tsaye tsayin Daka don gudun kai masa mamayar ba zata.
Ganau sun ce akan ga yan taaddar suna gewayar garin amma basu taba gangancin shiga garin ba.
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779.081377777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here