Muna goyon bayan Al-makura a takarar Sanata

0

Muna goyon bayan Al-makura a takarar Sanata

Inji Shugaban yan dako

Daga Zubairu Muhammad

Shugaban kungiyar yan dako na Qaramar hukumar Lafia dake Jihar Nasarawa
Alhaji Danji Muhammad Aliyu ya bayyana irin taimakon da Gwamna Umar Tanko
Al-makura yayiwa yan kasuwa masamman bangaren yan hatsi, ya bayyana haka ne
a yake zantawa da wakilinmu a ofishinsa dake Lafia.

Tunda farko Shugaban kungiyar Alhaji Danji Muhammad yayi kira ga alumman
Jihar Nasarawa da su fito kwai da kwarkwata wajen yankan katin zave saboda
katin zave abune mai mahimmanci ga mutum. Idan kanada katin  zave zai baka
damar ka zave duk xan takarar dakeso . kuma katin zave zai taimakamaka a
gurare dayawa .yanzu idan tafiya ta kama mutum idan wani abu ya faru koda
yan sanda sun kama mutum idan kana da katin zave zai tabbatar da kai xan
qasane kuma banki suna amfani da katin zave agurare dayawa yana amfanar da
mutum.
Ya kara da cewa yanzu zave yana karatowa idan mutum bayyanka katin zave ba
tayaya zai zave wanda yakeso.
Sanan yayi kira ga yan kungiyarsu ta yan Dako da su hanzarta su da iyalansu
suje su yanka katin zave saboda kuri’anka yancinka. Haka zalika yayi kira
ga Matasa dasu zage dantse wajen mallakar katin zave kuma su hanzarta wajen
bada mahimmanci da tsayawa takara ana damawa dasu tunda Shugaban qasa ya
tabbatar da cewa matasa suna iya tsayawa takarar Shugabancin qasa banga
dalilin da matasa zasu maida kansu baya su zama wadanda ake amfani dasu
wajen bangar siyasa saboda cigaban wani ba.
Suma su rika tsayawa takara ana damawa dasu saboda sune kashin bayan siyasa
a ko ina.

Haka zalika ,ya kara kira ga ya’yan kungiyar yan Dako da su kara kaimi
wajen shiga a dama dasu a siyasan qasa kamar yadda aka san tarihin
kungiyar, ya’yanta sun dade ana damawa dasu a siyasan Jihar. Cikin su akwai
masu rike da mukamai na Jam’iyyu yanzu haka . Akwai kuma Dalget masu zaven
yan takara kama daga gunduma zuwa Qaramar hukumar zuwa Jihar. Saboda haka
wanan kungiyar tana da rawar da zata taka a siyasan. Yan siyasa su sani
akwai rawar da kungiyarmu zata taka kuma duk Wanda zaiyi damu zamuyi dashi
saboda akwai ya’yan wanan kungiyar dayawa da sukayi karatu abinda muke
bukata shine idan Gwamnati zada dauki ma’aikata ta tuntube kungiyarmu muma
mu kawo ya’yan kungiyarmu wadanda sukayi karatu .
Ta hakane za’a rika rage masu zama a gari babu aikinyi . idan wani yaga
abokinsa wanda sukayi karatu ya samu aikin Gwamnati ta bangaren yan dako to
shima zaizo ya shiga wanan kungiyar saboda zaisa ran wata rana zai samu
aikin Gwamnati ko ta nan.
Muna da kuri’a munada masu zaven yan takara idan mukace ga wanda zamu zave
insha Allah sai kaga yakai ga Nasara.
Sanan yayi kira ga yan siyasa cewa su sani mu muna da kuri’a kuma zamuyi ne
da wanda zaiyi damu idan ka yarda da ka’idojinmu sai mu zave ka saboda
siyasa kowa na bukatar biyan bukatartane a lokacin da yake bukata .bazamu
zave mutum da yaci ya tafi mun daina ganinshi ba

See also  Wata mahajjaciyar Najeriya ta tsinci tsabar kudi har dala 80,000 a kasar Saudiyya.

Alhaji Danji Muhammad Aliyu ya yabawa Gwamna Umar Tanko Al-makura wajen
bubkasa harkan kasuwanci ta yadda ya samar da kasuwannin zamani a Jihar.
Ya kara da cewa Gwamnan ya taimakawa yan kasuna sai da hatsi inda ya samar
masu da matsuguni na dindindin ya kuma basu kudi saboda su gina wanan
shaguna.
Sanan yayi mana alkawarin gina mana ofishinmu a wanan gurin.
Sanan yayi kira ga yan kasuwa dasu kara hakuri ganin cewa wajen da suka
saba dashi zasu barshi.
Yace; suyi adu’a Allah yasa wancan wajen ya zama alheri garesu.

Yace; abinda Gwamna Al-makura yayi abin mu yaba masane.saboda tunda mukeyi
Gwamna a Jihar din nan bamu tabayin Gwamna kamar Al-makura ba.
Kuma mun dade muna jiransa daya fito takarar Sanata tunda yanzu Allah yasa
ya amince kuma ya bayyana kansa zaiyi.
To zamu bashi goyon baya saboda munsan za’ayi Sanatan da ba’atabayin
irinsaba a Jihar Nasarawa.

Da yake magana kan rikicin manoma da makiyaya Shugaban na yan Dako, yayi
kira ga Gwamnati data kara yawan Jami’an tsaro a guraren da ake fama da rikicin domin samun zaman Lafiya mai dorewa
Sanan yayi kira ga manoma da makiyaya su hakura da wanan rikicin saboda babu abinda yake haifarwa face zubar da jini da dumbin asara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here