MURNAR SAUYA SARKI: RARARA ZAI RABA MOTOCI DA KUJERUN MAKKAH

0

MURNAR SAUYA SARKI: RARARA ZAI RABA MOTOCI DA KUJERUN MAKKAH.

Saboda shauƙin cire Sarkin Kano Muhammadu Sanusi da maye gurbin sa da Aminu Ado Bayero, fitaccen mawaƙin nan Dauda Kahutu (Rarara) ya saka gasa inda zai raba kujerun Makka da Umara da motoci, da kuɗaɗe kyauta ga waɗanda su ka yi nasara.

Rarara ya bayyana haka ne a wani saƙon bidiyo da ya fitar a shafin sa na YouTube.

Ya ce ya saka gasar ne don nuna farin ciki game da naɗa Aminu Ado Bayero a matsayin Sarkin Kano da gwamnatin jihar ta yi.

Rarara mawaƙin siyasa ne wanda ke bin gwamnatin da ke kan mulki.

Ya ce a ƙa’idojin shiga gasar ana so duk wani mawaƙin Hausa da ya ke Nijeriya ko wajen ta da ya yi sabuwar waƙa ga sababbin sarakunan Kano guda biyar, wato na Kano da na Bichi da na Ƙaraye da na Sarkin Gaya da na Rano.

A ƙa’idojin, ana so kada waƙar ta wuce minti biyar, sannan ya kasance a cikin minti biyar ɗin nan mawaƙi zai yi wa kowane sarki waƙar sa, cikin salo da zai burge kowace fada, da kuma su kan su sarakunan.

See also  Sama da mutane dubu Ukku da Dari biyar ne Suka Sauya Sheƙar Daga PDP Zuwa Jam'iyyar APC karamar hukumar charanchi

Wata ƙa’idar ita ce tilas ne duk mawaƙin da zai shiga gasar ya kasance ya na da rajista da Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano.

Bugu da ƙari, mutum 50 kacal za a zaɓa zaba a matsayin zakarun gasar.

A cewar sa, a ranar da za a fidda zakarun kowane mawaƙi zai zo da waƙar sa a rubuce kuma ya rera ta a gaban manyan baƙin da za su halarci taron, cikin su har da Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

Rarara ya bayyana cewa ya tanadi farfesoshin nazarin harshen Hausa da za su zama alƙalan gasar.

Ga jerin sunayen kyaututtukan da zai ba waɗanda su ka yi nasara:

Na 1: Mota
Na 2: Mota
Na 3: Kujerar Makka
Na 4: Kujerar Makka
Na 5: Kujerar Umara
Na 6: Kujerar Umara
Na 7: Keke Napep
Na 8: Keke Napep
Na 9: Babur
Na 10: Babur.

Sauran mawaƙan 40 kuma kowannen su za a ba shi kyautar N100,000

Za a iya tura wakokin ta wannan lambar a WhatsApp. 07067090960
Ko kuma ta email: @adamfilms2020@gmail.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here