MUTANEN DAJI MASU DAUKE DA MAKAMAI NA YADDA SUKE SO

0

MUTANEN DAJI MASU DAUKE DA MAKAMAI NA YADDA SUKE SO
Daga jaridar taskar labarai

A ranar Talata 31/03/2020 da misalin 8:00am na safe wasu da ake zaton dakarun daji ne, sanye da kayan fulani akan babura kirarar boko haram su biyar dauke da goyon mutum daya-daya jimla su goma kenan, dukkan su dauke da adduna da sanduna. Suka afka gidan wani babban Mallamin addinin musulunci mai suna Mallam Isah a gidansa dake Giyaye wasu gidajen gona dake gabas ga kauyen Shirgi, cikin yankin karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina.

Shi dai wannan bawan Allah ana ikirarin cewa babu wani makarancin alkur’ani da ya kai shi sani a yankin su. Suna isa basu yi wata wata ba sai suka kama dukan shi, wani makusancin shi yazo domin kawo masa dauki shima suka yi cikin sa, harma wani daga cikin su yana cewa ku sa mashi adda mana, ganin haka ne yasa ya gudu domin tsira da rayuwar shi.

Daga bisani kuma sun shiga dakunan matansa sun kwashe kudi da sauran abubuwa, sannan suka kama tumaki guda bakwai suka yi awon gaba da su tare da shi Malamin.

Da kura ta nutsa Iyalan Malamin sun nemi jin dalilin yi masu wannan zalunci, da yake sun gane mutanen da suka aikata ta’addancin, sai aka bayyana masu cewa wai wata yarinya ce bata da lafiya aka ji tana ambaton sunan shi, domin haka suka tafi da shi daji da nufin sai ya tsallaka ta.

See also  RIKAKKEN DAN TADDA : ALHAJI HAMISU BALA WADUME.

Kuma ita wannan marar lafiya diya ce gare shi, sannan ya shafe watanni bai sa ta ido ba domin ba yanki daya suke ba.

Da suka kai shi daji, sun bukaci ya tsallaka ta, amma yace lalle shi bazai tsallaka ta ba, suka ce za su kashe shi, yace masu tafi nono fari, dalilin da yasa suka aiwatar da kudirin su ba tare da wani bata lokaci ba.

Dangin shi sun bukaci a basu gawar domin yi masa sutura, amma suka hana su, suka ce wai tuni sun rufe gawar, daga karshe dai sun basu tumaki guda biyar cikin bakwai da suka dauka.

A wani labari makamancin wannan da ya faru a kauyen Watangadiya dake yammacin Batsari (2km daga Batsari), cikin makon da ya gabata, anga dakarun na daji kan babura rataye da makaman su, sun kai samame gidan wani Mallam Hamza, inda suka yi awon gaba da shi da matar shi.

Amma daga bisani bayan an sako su sun dawo gida, sai suka bayyana cewa wata matar Dan shi ce ke bata da lafiya, shine ake zargin kishiyar ta ce tayi mata asiri.

Wannan dalilin yasa aka yi masa tarar N200,000.00, shima bokan da ake zargin yayi asirin anyi masa tarar N200,000.00 da alkawalin zai warkar da matar da bata da lafiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here