Mutun biyu sun rasa ransu wurin taron rufe yakin Neman zabe a Zamfara
Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau
A kokarin gudanar da taron yakin Neman zaben da jam’iyar PDP da APC suke kokarin yi a karamar hukumar Bakura , mutun biyu sun rasa ransu sakamakon artabu a tsakanin magoya bayansu.
Mutuwar matasan biyu ya biyo bayan sanya taron ne a rana guda da kowace jam’iyar tayi ,na sanya ranar alhamis 3/12/2020 a matsalayin ranar rufewa.
Sai dai shugaban hukumar ‘yansanda mai kula da yankin sokoto ,Kebbi da zamfara, AIG Muhammad A mustafa ya bada umurnin dakatar da taron rufe yakin Neman zaben na Bakura.
Da yake yiwa manema labarai bayani, ya kara da cewa ganin yadda taron yazo da matsaloli wanda ya kai da rasa rayuka hakan yasa suka bada umurnin dage taron
Sai dai sakamakon yadda abubuwa suka rincabe yasa gwamnantin jihar zamfara ta kafa dokar ta baci na awa ashirin da hudu, Wanda zai dauki tsawon kwana biyu, daga ranar alhamis zuwa jumu’a, kuma dokar zata shafi karamar hukumar Talatar mafara CE da kuma karamar hukumar Bakura, Sai dai an bayyana cewa wannan dokar ba zai hana gudanar da zaben ba a ranar asabar mai zuwa.
Duk da wannan umurni be hana jam’iyar APC karkashin jagorancin Abdul’aziz Yari sun gudanar da taronsu ba , Wanda daga bisani tsohon gwamnan jihar zamfara, Alh Abdul’aziz Yari ya rufe taron .
Duk da umurnin da AIG ya bada na dage taron da dokar da gwamnati ta sanya be hana jam’iyar PDP itama ta gudanar da nata taron ba, zuwa lokacin hada wannan labarin dai gwamnan jihar zamfara, Hon Bello Muhammad matawalle ya tunkari karamar hukumar Bakura don gudanar da nasu taron jam’iyar ta PDP.