NAZIRU YA YI MURABUS. WA ZA YA MAYE GURBIN SA?
Daga shafin Kannywood Exclusive
Fitaccen mawakin Sarautar nan mai suna Naziru M. Ahmad wanda ake yi wa lakabi da ‘Sarkin Wakar Sarkin Kano’ ya yi murabus.
Mawakin ya rubuta takardar yin Murabus din ne a ranar Juma’ar da ta gabata, 13 ga wannan watan na Maris.
Mai Martaba Tsohon Sarkin Kano Malam Sunusi Lamido Sunusi II shi ne ya nada Naziru a matsayin Sarkin Wakar Sarkin Kano a ranar 27 ga watan Disamba 2018.
Murabus din na Naziru baya rasa nasaba da tube wanda ya yi masa saurautar da gwamnatin jihar Kano ta yi. Tsohon Sarkin Wakar Sarkin Kano ya kwashe kwanaki 435 yana sarautar sa. Tun kafin Sunusi Lamido Sunusi II ya zama Sarkin Kano Naziru yana daya daga cikin mawakan sa da suka dade a tare.
Bayan Murabus din Naziru, sai kuma kallo ya koma sama wurin ganin mawakin da zai maye gurbin sauratar Naziru.
A wani binciken da ‘Kannywood Exclusive’ ta yi ta gano sarautar ba za ta wuce mawaka biyu ba, ko dai Aminu Ladan Abubakar (Alan Waka) ko kuma Dauda Kahutu Rarara. Dukkan mawakan kowa ya baje kolin basirar sa wurin yi sabuwar wakar ta ya sabon Sarki murna. Kamar yadda suka yi masa a lokacin da yana Sarautar Bichi.
Mawakan biyu su kasance dukkan su mawaka ne ga sabon Sarkin Kano Aminu Ado Bayero. In dai ba a manta ba, a ranar 13 ga watan Agusta 2019 mai martaba Aminu Ado Bayero, a lokacin yana Sarkin Bichi, ya yi bikin nada Alan Waka a matsayin Dan Amanar Bichi. Wanda kuma shi ne nadin Sarauta ta farko da Sarkin na Bichi ya yi tun bayan lokacin da Gwamnatin Jihar Kano, ta amince da nada shi a matsayin Sarkin na Bichi kafin ya zama Sarkin Kano.
A ganin ku tsakanin Rarara da Alan Waka wa zai samu Sarauta a masarautar Sarkin Kano, ko kuwa kowa zai samu ta shi ta daban?