OYO| Jima’an Amotekun Sun Kashe Fulani 7 A Ibarapa

0

OYO| Jima’an Amotekun Sun Kashe Fulani 7 A Ibarapa

Wasu jami’an Hukumar Tsaro ta Jihar Oyo da aka fi sani da Operation Amotekun sun Kashe Wasu Fulani makiyaya a Aiyete da ke karamar Hukumar Ibarapa ta Arewa a jihar.

Lamarin ya fara ne a kauyen Okebi da safiyar ranar Asabar amma ba a iya gano musabbabin abin da ya faru ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Wani Mai suna Saliu, wanda ya ce shi mazaunin yankin ne ya shaida wa wakilinmu cewa an kashe mutane bakwai, sannan Kuma kimanin gidaje bakwai aka kona kurmus.

Saliu ya ce, “An kashe Alhaji Usman Okebi tare da ‘ya’yansa maza guda biyu. Ba mu san abin da ya haifar da fadan ba. An harbi wasu mutane kuma sun ji rauni.

See also  ƁULLOWAR BAREBARI LARDIN ZAZZAU DA KAFA GARIN BARNAWA DA SAMUWAR GIDAN MALLAWA DA GIDAN BAREBARI (2).

Wata majiyar kuma ta ce an yi artabu ne tsakanin jami’an Amotekun da Fulani Bororo, ya ce an kashe wasu mutane amma ba zai iya cewa ga wadanda suka yi asara mai yawa ba.

Kwamandan Amotekun a jihar Oyo, Kanal Olayinka Olayanju (mai ritaya), lokacin da aka tuntube shi ya ce yana kan hanyarsa ta zuwa wurin don bincika abin da ya faru.

Jami’in hulda da jama’a na Rundunar ‘yan sanda a jihar Oyo, Mista Olugbenga Fadeyi, lokacin da wakilinmu ya tuntube shi ya ce ya tuntubi DPO din da ke reshen’ na Aiyete yana wurin don gano abin da ya faru.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here